Hanyoyin Yanda Zakubi Ku Rabu Da Kaushin Kafa Da Faso Cikin Sauki Musamman A Lokacin Sanyin Nan

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku a wannan shafi namu Mai albarka na arewamusix.com

Yanda zaku rabu da kaushin kafa koh faso:

Shi tafin kafarmu na daya daga cikin sassan jikinmu da ya kamata mu rika kulawa da shi akai-akai, kasancewar idan ba a yi hanzarin magance kaushin kafa ba, sai ya zarce yakoma faso.

Ta Yanda Zaki Gane Kinada Kaushin Kafa:

Daga lokacin da kika fara jin tafin kafarki na janyo audugar jikin kujerar daki ko bargon da kike lullubuwa da shi, ko kuma yana kama kaya koh yana gogar jikinki, idan kika ji haka toh koh lallai alaihin kina da kaushin kafa.

KU SHIGA KUGA JERIN KALOLIN RUWAN DAKE FITA DAGA FARJIN MACE DA YADDA ZAKUYI MAGANIN SU

Mutane da dama na son rabuwa da wannan matsalar ta Kaushin Kafa, a dalilin hakan yasa muka kawo muku hanyoyin da zaku bi don rabuwa da kaushin kafan da yardar Allah.

  1. Ki zuba ruwan dumi a cikin bokiti koh wani abun mai fadi, sannan ki sanya kafarki a cikinshi.
  2. Bayan tafin kafarki ya juku a ciki, sai ki cire daga cikin ruwan dumin, daga nan ki dauki dutsen goge kafa, sannan ki rinka goge tafin kafarki wurin da yake da kaushin, ki rika zagaya dutsen a wuraren da kaushin ya fito, daga nan ki sake mayar da kafar taki cikin ruwan dumin.
  3. Bayan yayi kamar minti 15 sai ki sake goge tafin kafarki da dutsen goge kafar domin cire fatar da ta mutu a tafin kafarki taki.
  4. Toh daga nan sai ki wanke tafin kafarki da sabulu a cikin ruwa, sannan sai ki cire kafarki, ki goge da tawul dinki Mai tsafta
  5. Daga nan ki shafa man tafin kafa, idan ba ki da shi sai ki shafa man baseline.
  6. Idan kika gama sai ki dauko safanki ki Sanya, sannan ki sanya kafarki a cikin leda, bayan kin daure sai ki kwanta barci. Zaki barshi baza ki kwance ba sai washegarin rananr.

Yanda Ake Gyaran Kafa:

SHIGA KIGA YADDA ZAKI GYARA NONONKI

  1. Gishiri da shampoo: dafarko zaki samu ruwan dumi dai-dai yadda bazaki kona kafarkiba, kizuba shampoo da gishiri acikin ruwan, kisanya kafafunki aciki natsawon minti shabiyar. Sannan saiki wanke kafar tas idan ta bushe saiki shafa man zaitun.
  2. Man kwakwa da man ridi: Zaki samu kihadasu waje daya kicakuda, dadaddare ki dauko kishafa akafafunki kisanya safa akafar zuwa safe, saiki wanke da ruwan dumi, idan yabushe kishafa man zaitun ko man ridi.
  3. Man danyen man shanu da man alayyadi: Ki hadasu waje daya kitabbatar sun hade jikinsu sannan ki shafa akafarki dadaddare zuwa safe in shaa Allahu baki ba kaushin kafa saidai kiga wasu sunayi Amma ke bandake.

Ayi share domin ‘yan uwa su amfana.

Apply Now

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button