Wasu Daga Cikin Matsalolin Da Mata Ke Fuskanta Da Family Planning Tare Da Maganinsu:
Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu Mai albarka na arewamusix.com
Ayau rubutun nawa yazo muku da wani salo ne na tambaya da amsa, abinda nayi hakan kuwa badon kowa bane sai donku masu bibiyar shafin nan namu mai albarka, sannan kuma inason ku fahimci bayanin nawa dakyau hakan ne yasa nazo muku da wannan salon
Ga tambayoyin da amsoshinsu nan na jero muku su har guda goma sha biyar (15) Ina fatan zaku fahimta yanda Yakamata sannan don Allah idan kun gama kuturawa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.
- Likita nakan fuskanci amai da tashin zuciya a yayin dana sha magunguna na na hana daukar ciki wato Oral Contraceptive pills. Menene abun yi likita ?
Amsa: A wasu duk da ba duk ba sukan fuskanci tabbas abunda muke kira Nausea/vomiting… toh amma duk da haka babu bukatar sai anba mutum maganin hana tashin zuciya, kusan normal ne, physiologic response ne, ba abun tsoro bane. Amma ana iya shawartar Mace idan da akwai abunda ke sa tashin zuciyar ya lafa toh tayi. Misali a iya dangwalar gishiri a lasa atsakiyar harshe, ko asami lemon tsami kadan a matsa abaki, da sauransu.
- Bayan Nasha Maganina na tazara (OCP’s) ba afi awa 2 ba, sakamakon tashin zuciya sai nai amai! Shin me ya kamata nayi?
Amsa: Zaki kuma daukar wani maganin ki kuma sha ne, matukar ba’a sami awa 3 zuwa 4 da shan ba.
Idan kuma kika dada yin amai, toh ki bayani sai likitanki ya canza miki da magani suppository wanda ake sawa cikin farji ya shiga ciki shikenan.
- Likita OCP’s dinnan kullum ne ake sha, toh amma yanzu gashi kullum sai ya sani amai inna sha. Me ya kamata nayi?
Amsa: Abunyi shine likitanki ya rubuta miki magani suppository na sakawa cikin farji. Akyale sha ta bakin, inkuma na farji na hanaki sakewa toh a canza miki zuwa Emergency Contraceptive wanda yake progestin ne kurum.
- Haila ta na rikicewa yayin amfani da maganin sha na OCP’s ko Progetin only pills… Ya kenan??
Amsa: Babu bukatar wani magani, kurum shawarwari za adan ba mutum akan yadda zaike zamowa cikin shiri game da hakan… Saide in abun ya cigaba kuma akaga jinin ya zamo yadda baza a iya jurewa ba toh ki koma a dakatar da shan maganin… likitan ya taimaka miki wajen za6ar wata hanyar.
- Nima ina amfani da maganin ne Allura toh amma nima haila kan rikice, ko kuma nake ganin Jini atsakanin haila wato spotting!
Amsa: Ganin spotting yawanci na faruwa dama musamman bayan allurar farko, wato tashin farko na soma amfani da abun ba abun damuwa. Shawarwari kurum kike bukata
Idan duk bayan haka ya cigaba jinin bai dena ba. Toh akwai bukatar ai miki Gynecological exam aduba cikin farjin akwai yiwuwar matsalar ba daga maganin bane kila akwai inflammation a cervix din, ko wani ciwom dake iya yaduwa wato STI ko mace nada PID.
- Nima Allura nake amma yanayin fitar jinin ya karu sosai is Heavy! Ya kenan?
Amsa: ana iya rubuta miki magani rukunin Hemostatic agents domin tsaida shi ya saitu
Idan duk bayan baki magani jinin bai dena ba… Toh akwai bukatar ai miki Gynecological exam aduba cikin farjin akwai yiwuwar matsalar ba daga maganin bane kila akwai inflammation a cervix din, ko wani ciwom dake iya yaduwa wato STI ko mace nada PID.
Idan ba aga wata matsala ba toh sai acanza wata hanyar.
Sannan kuma a iya hadamiki da magani IRON ki rika sha domin gujewa fuskantar matsalar karancin jini.
- Ni kuma likita implanon aka saka mun amma Al’adata na rikicewa, ko kuma na rika ganin jini batare da ina cikin haila ba.
Amsa: Ganin spotting shima normal ne ga implants musamman a shekarar farko. Amma akwai bukatar ai miki Vaginal examination idan babu wata matsala da aka gani dake nuna kila ko itace dalilin jinin toh likita na iya rubuta miki magani rukunin NSAIDs domin tsaida shi, ko kula low dose oral contraceptive musamman Ethi, bazan fadi cikakken sunan ba domin magani ne da likita kadai ke rubutashi, in anje masa da korafi.
Idan hakan bai tsaida jinin yasa haila.ta saitu ba toh sai acanza wata method din ta planning.
- Ni kuma jini nake gani Spotting bayan ansanya mun robar cikin mahaifa wato IUD… Me hakan ke nufi?
Amsa: Spotting a wacce aka sama IUD shima normal ne a watanni 3 zuwa 6 da sawa… musamman Copper IUD
Idan kinga duk da haka kinsaon magani; toh ki magani likita zai rubuta miki NSAIDS (Banda Aspirin) da zaki sha aranar da kika fara haila.
Idan duk da haka jinin ya cigaba toh aduba wata hanyar ta planning ai canji.
- Likita nima IUD din ne aka samun amma Hailar Heavy take zuwa jinin na mun rushing…. ya zanyi?
Amsa: Shima rushing bai zama illah, musamman watanni 5 na farko kuma in akai hakuri daga wata 6 yana denawa ya saisaitu da kansa hakan na faruwane sakamakon abunda aka saka bakone agurin kuma gashi yana sakin sinadaran da gurin bai saba jinsu ba.
Amma in duk da haka ana takura saboda yawan canza pants da kuma kasala saboda zubar jinin toh ai magana da likita… zai rubuta NSAIDs ko kuma Heomostatic Agents irinsu (trx a……), amma akowanne irin fitar jini kara amanta kar a kuskura ai amfani da Aspirin domin tsinka jini yake duk da NSAIDs ne saide zubar jinin ya karu.
Ana iya ba Mace sinadarin IRON saboda jinin da take fitarwa… gudun anemia… idan duk da haka jinin bai tsaya ba to acanza wata hanyar acire IUD din
- Likita menene abin yi ansa mun IUD amma yanzu ta tabbata inada ciki?
Amsa: Gwajin ciki ta fitsari ko jini kadai bai wadatar da tabbas akwai ciki ba, don haka abu na gaba shine arubuta ultrasound domin a tabbatar in ma da cikin to a tabbatar ba a wajen mahaifa yake ba wato ECTOPIC, tunda ko a wajen mahaifa ciki yake pregnancy test duk postive za aita gani.
Idan cikine sosai acikin mahaifa toh sai likita yai bayani game da illar barin “IUD” din yana iya haddasa 6ari wato miscarriage a watanni uku na farkon cikin ko kuma watanni uku na tsakiya (second trimester).
Amma inta yadda cire “IUD” din zai rage wancan hatsarin…
Amma in duk da haka mace tace ita de tana jin tsoron kar ata6a mata ciki abarshi… toh afadamata de akwai yiwuwar yin 6arin duk da haka, sannan tana iya haduwa da sepsis wato infection da zai shiga jininta zuwa ko kuma barazana ne ga rayuwarta. Don haka in anbarshi duk sanda taji ciwon mara, ko jini na fita sosai, ko murdawar ciki tai maza ta taho ga likita…
Inkuma larura ce tun farko tasa… don haka baza a iya barin cikin ba… toh nan ma likita zai fadamata abun da ya kamata a irin wannan lokacin.
- Likita Anzo Cire “IUD” Sakamakon ciki da ya bayyana amma ba’a ga IUD din ba ya shige ciki shin ya kenan?
Amsa: Likita zaisa ai ultrasounded yana tsaye za ai za’aga inda IUD din yake kuma zai amfani da kwarewarsa ya cirosa… idan kuma duk da haka bazai ciru ba toh za asa ido akai akai arika bibiyar mai cikin babu abun damuwa tunda jariri na jujjuyawa wataran zai dawo angle din da IUD din zai ciru.
12. Tambaya: Likita ni kuma Implants na saka amma gashi ciki ya bayyana a jikina?
Amsa: Eh ana samun haka musamman in yai shekara 2 ko 3 ya zamto yai expire akan kari sakamakon yadda akai tsammani, ko kuma mace nashan maganin gargajiya kona asibiti wanda yake rage masa inganci kamar yadda na fada a daya post dina musamman masu shan maganin Farfadiya ko Anti fungal
Abinyi shin sai acire implant din shikenan.
- Tambaya: Likita ansamun “IUD” amma gashi naje asibiti sakamakon ciwon mara ko ganin farin ruwa anyi gwaji ance ina da P.I.D. Ya kenan?
Amsa: Abunyi shine za’a bar IUD din abaki antibiotics maganin PID din, sannan mijinki ma bashi magani rigakafi, idan duk da haka baki rabu da PID din ba sai acanza wani maganin, ko adau sample na duscharge din agwada agano kwayar cutar abaki magani kai tsaye… inko bayan haka baki rabu da PID din ba toh sai acire PID din akuma treating din PID din. Bayan kin warke a mayar ko acanza miki wata hanyar planning din.
- Tambaya: Likita idan bayan amfani da hanyar planning bayan ancire amma kuma ciki yai wuyar samuwa menene abun yi?
Amsa: Hakan na daga side effects na planning musamman allura koma implanon don haka ba abun damuwa wani lokacin ana iya kuma shekara batare da ciki ba. Wani bun shekara 2, suna da wata halayya saboda jikin mu ya bambanta wasu in sun planning toh jikinsu sai yai double… na wata 6 sai ya qara wata 6, na shekara 1 sai ya kara shekara.
Amma de in damu da sami haihuwa to aje wajen likita idan aka tabbatar mace na ovulating shikenan kurum ai hakuri yana nan tafekomi normal
- Tambaya: likita wacce shawara zaka ba wadanda basu fara tara iyali ba amma suna son planning musamman amare?
Amsa: Amare kan so aja love kafin akaiga ciki tunda akwai 50% chance na samun ciki a watanni uku na farkon aure, ada akanyi tunanin fara planning kafin haihuwa ko cikin fari akwai matsala amma de sabon trial din da aka gabatar duk masa sun kore haka… ana iya fara planning ako yaushe.
Shawara ta anan shine: a likitance dai bawata illa don anfara planning batare da anhaihu koh sau daya ba, babu wani binkicen da ya nuna matsala akan hakan, hasalima yawancin models da celebrities din nan cikin mawakan Mata da sauransu da kuke gani na duniya haka suke; sai daga baya in sun shirya haihuwa tukun.
Amma don cire ko kwanto da samun natsuwa a shawarce ku jaraba amfani da Billing method wato “CALENDAR METHOD” Wato kasan adadin kwanakin hailar matar take da kuma kwanakin da take, saiku ke tsallake kwanakin da akasan baza a riski Ovulation ba.
Wato ita mai haila duk bayan sati 4 (28 days) ta kauracewa saduwa bayan kwana 11 da daukewar haila har sai ranar 16, kunga an tsallake kwana 6 batare da jima’i ba tunda ovulation galibi kan faru exactly sati 2 bayan al’adane kunga 28Ă·2= 14, Day 14 ovulation
Idan mace mai yin haila duk bayan sati 3 ce wato kwana 21, toh da ta sami sati 1 da kammala period 21Ă·2= 10.5, kaga kenan ovulation bayan kwana 10, don haka kwana 3 kafin ovukation zai kama ranar 7 wato sati daya da gama haila sai a kauracewa saduwa tun bayan sati 1 da gama haila har sai ranar 13 kunga kenan kwana 6 kuka tsallake babu jima’i, daga nan sai acigaba da komi ba matsala
Inkuma bazaku iya hakuri ba duk da lokacin ovulation wani bin sannan ma mace tafi jin bukatuwa ga namiji toh a irin wadannan kwanakin da muke kira “wet days” sai ai amfani da condom in sun shiga ankoma “dry days” sai kuci cigaba da harkokinku yanda kuka Saba.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa suma su amfana.