Yanda Mace Zatayi Gyaran Gashi Da Ruwan Shinkafa Domin Samun Tsayin Gashi Da Laushi Da Tsantsi Hadi Da Sheki A Lokacin Sanyi

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi Mai albarka na arewamusix.com

Shin koh kin san cewa wanke gashinki da ruwan da aka wanke shinkafa yana kara abubuwa da dama wanda baki sansu ba?

Ruwan da aka wanke shinkafa da shi yana da sinadarai masu yawa dake kara wa gashi tsayi, kyau da kuma laushi.

Zaki iya wanke gashinki da ruwan shinkafa sau daya a sati domin samun wannan sakamakon.

Ga matakan da zakibi wajen wanke gashinki da ruwan shinkafa kamar haka:

Zaki samu shinkafar ki ma kyau, gwangwani daya koh kuma duk yadda kike soya zama, saiki zuba wa shinkafar ruwa ki bar ta ta jiku na tsawon minti ashirin koh minti talatin, saiki rinka yawan juya shinkafar saboda kar ta dunkule miki, toh idan ruwan ya koma launin ruwan madara hakan na nuna miki cewa yayi yanda ake so, daga nan saiki tace ki raba ruwan da shinkafar, saiki jika gashinki a cikin ruwan, in zai yiwu ki bar
shi ya jiku kamar tsawon minti talatin zuwa minti arba’in.

Bayan kin barshi yayi wannan mintocin, saiki wanke gashinki da ruwan sanyi ki taje shi har sai kin tabbatar duk wani abun shinkafar ya fita daga kanki, sannan sai ki daure gashinki.

Indai kikayi hakan toh zako kiga abin mamaki.

Wadannan su ne matakan da ake bi wajen wanke gashi da ruwan shinkafa.

Yanda Zaki Gyaran Gashinki:


Sanyi yana daya daga cikin yanayi da dalilin da ke zubar da gashin mace, saboda haka ya kamata mu kula da gashin kanmu, domin yana daya daga cikin abin dake dadawa mace kyau, akwai mayuka da dama wadanda ake shafawa a gashi don hana gashin zubewa, sannan akawai man zaituun da man kasto (castor oil), zaki iya hada man zaituun da zuma koh ruwan lemun tsami da man kwa-kwa, wadannan mayukan na gyara gashi da hana shi zubewa, ya sanya shi sheki da kuma tsayi, man zaituun yana da kyau a rinka shafashi a gashi domin kare shi daga bushewa, zaki iya sanya zaituun a wuta koh a rana, idan ya narke (sosai) sai a shafa a fatar kai, rashin shafa man zaituun a fatar gashi na sanya gashin karyewa.

Man kasto (castor oil) don gyaran gashi: Zaki iya samun wannan man a shagunan da ake sayar da kayan kwalliya a kasuwa, zaki narkar da man a rana, sannan saiki turara tawul din wanka, bayan kin shafa man, sai ki daura tawul din a kai har na tsawon mintuna goma sha biyarkafin ki wanke.

Man zaituun da zuma: Zaki hada cokula uku na zuma da man zaituun ki motsa (ya hadu sosai), sannan saiki shafa a gashi, bayan โ€™yan mintuna kadan, kamar misali minti goma, saiki wanke da man wanke gashi.

Ruwan lemun tsami da man kwa-kwa: Zaki matse ruwan lemun tsamin, saiki gauraye da man kwa-kwa, sannan saiki shafa a fatar kai kafin a wanke.

Ayi share domin sauran ‘yan uwa su amfana.

Apply Now

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

One Comment

  1. Your blog is a constant source of inspiration for me. Your passion for your subject matter shines through in every post, and it’s clear that you genuinely care about making a positive impact on your readers.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button