Kadan Daga Cikin Amfanin Da Magungunan Da Lemongrass Keyi Ga Lafiya:
Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na arewamusix.com
Lemongrass wato (Cymbopogon citratus) wata shuka ce mai dadin kamshi, wato wata irin ciyawace doguwa mai launin kore da kamshin lemun-zaki, kuma duk da yake dai bata da alaka da lemun-zaki, kamshin ciyawar mai karfi da dandano yayi kama dana lemun-zaki (saidai kuma ita bata da zaki), ana samun ciyawar a kasashe masu yanayin zafi koh kuma yanayin dumi, sannan anfi yawan amfani da ita a kasashen Asiya, Afurka da Australia kuma anfi yawan amfani da wannan ciyawa a kasashen Asiya wajen girki, a kasar Indiya kuma akanyi amfani da ita a matsayin maganin gargajiya (herb), Kuma na amfani da busasshiyar ciyawar koh danyarta domin amfani na daban-daban, kuma anfi amfani da ita wajen hada shayi , miya koh kori (curry) domin ta zamo hadin kayan kamshin girki. Ana samun manta (lemongrass oil) a kasuwa wanda shima ake amfani dashi na daban-daban.
Amfanin Da Lemongrass Takeyi Ga Lafiya:
Zai iya yiwuwa kana da wannan shuka a cikin gidanka koh a lambunka koh kuma kana amfani da ita, toh amma baka san ainahin amfaninta taba ga lafiya ba kawai dai ka dauketa a matsayin shuka ce domin k’awata gida, koh filebo maisa kamshi a kofin shayin koh a lokacinda kake kurÉ“awa. Toh ka bude idanunka, domin kuwa wannan ciyawa amfaninta ya wuce na adon gida kadai koh kamshin shayinka da kake jin dadin sha saboda dandano da kamshin da take baka a lokacin da kayi amfani da ita.
Ciyawar Lemongrass nada ado da zata iya yima lafiyarka domin inganta ta, wasu daga cikin amfanin wannan ciyawa mai albarka sun hada da:
- Tana bada kariya daga ciwon-daji/kansa wato (Anti-cancer). Shukar lemongrass nada sinadarai masu kamshi na “citral”, wanda binciken kimiyya ya nuna cewa yana kashe kwayoyin halitta da ciwon kansa ya harba a jiki (cancer cells). Haka kuma yana inganta lafiyar kwayoyin halittar jiki gaba daya (improving cellular health).
- Yana karin-jini da hana rashin-jini (Anaemia). Lemongrass nada sinadarin “iron” mai yawa, wato sinadari maisa karin-jini domin cikakkiyar lafiya da kuma hana wasu matsalolin na rashin jini.
- Yana rage hawan-jini (Reducing high blood pressure). Yawan sinadarin “potessium” a cikin lemongrass, sinadarin mai inganta lafiyar zuciya, koda da sauran sassan jiki, na taimakawa wajen hana hawan-jini, cututtukan zuciya, mutuwar sashen jiki, ciwo kansa, matsalolin rashin narkewar abinci da rashin haihuwa, cikin yardar Allah duk yana ragewa.
- Yana bada kariya da hana girman kananun halittu masu haddasa cututtuka a jiki (Anti-septic) da kuma hana kumburi, wuri yayi ja, da radadin ciwo a jiki (Anti-imflammatory), musamman taimako ce ga masu ciwon gabobi da sassan jiki da sauransu (gout, arthritis).
- Sannan yana yaki da cututtukan bakteriya dana fangas wato (Anti-bacterial and anti-fungal) saboda haka tana maganin zazzabin cizon-sauro da taifot (Malaria and typhoid) da sauransu. Haka kuma, tana maganin cin-ruwa na yatsun kafa da makero shi kuma amfani zakuyi da manta da sauransu ( athlete’s foot, ringworm).
- Yana maganin mura, zubar hanci da hawaye, kaikayin ido, atishawa, toshewar hanci (Cold,flue and hay fever) da dai sauransu.
- Yana tace duk wani abu mai guba dake jiki, musamman na abinci, koh wani abu mai cutarwa da fitar dasu daga jiki (Detoxifying), sannan tana tsaftace hanta, koda, mafitsara dadai sauransu.
- Kuma tana inganta bacci / yakar da rashin bacci wato (Fighting insomnia). lemongrass nada tasiri wajen kwantar da hankali da fada da rashin bacci domin samun cikakkiyar lafiya.
- Sannan tana taimakawa ga masu ciwon-suga wato (Diabetes). Tana rage yawan suga cikin jini, tsarkake saifa da inganta aikinta.
- Sannan kuma tana inganta kwakwalwa wato (Improving nervous system). Lemongrass na taimakawa kwakwalwa wajen maida hankali don lakantar karatu, rike karatun da kuma taimakawa wajen sarrafa karatun/ilimi, sinadarin “magnesium”, “phosphorus” da “folate” da ake samu a cikin ciyawar nada tasirin kyautata lafiyar kwakwalwa
- Yana rage kiba wato (Weight loss), shan lemongrass musamman a shayi na narkarda kitse, Kuma tana sanya yin fitsari akai-akai a lokacinda take fitar da duk wani abu mai yawa da jiki baya bukata wanda zai iya cutar da lafiya.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.