Wasu Daga Cikin Illolin Da Daurin Kirji Ke Haifarwa Mata:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na arewamusix.com

Illolin Daurin Kirji Ga Mata:

Wai shin menene ma
Daurin Kirjin?

Shi daurin Kirji shine wanda mata keyi a kullum idan sun fito daga wanka, in dai haka ne ma’anarsa ashe toh bai kamata ya fi minti 5 a kirjin mace ba, domin yana da illolin da dama ga Kadan daga cikinsu.

  • Yana Saka nonon mace ya zube da saurin ya zama tamkar silifas koda kuwa budurwa ce.
  • Yana sa ciwon kirji saboda danne jijiyoyin hanyar jinin da suke biyowa ta saman nononta data tamke kashin kirjin.
  • Yana sa miji ya rinka yi miki kallon gargajiya koh kuma wata bagidajiya.
  • Sannan yana sa zubewar mutunci ranar da zani ya fadi a gaban mutane.
  • Yana sa kiji kunya a duk ranar da daya daga cikin yayanki suka cire miki zanin.

Mata idan da hali ku nemi rigar nan da ake sakawa bayan gama wanka saboda kulawa da nono domin abune muhimmi a gurin ‘ya mace data san kanta, macen data san kanta mana, ai itace ta damu da kirjinta Kuma take kula da tattalinsu domin shine kuwa shine damuwar kowane da namiji koh da kuwa ace mijinki baya miki magana a kansu, toh ki sani a cikin zuciyar sa dole ya damu, domin idan nonuwanki sun fara bacci lallai ki tabbatar idan za’ayi miki dinki a yi miki dinki mai gida (bra) saboda a basu hakkin su da fatan zamu kula mu daina yin daurin kirjin, idan kuma anki toh kina zaune zakiga wata sabuwar ‘yar shekara 17 yazo da ita ya aura abarshi.

Ki Kula Da Nononki:

Nono wani bangare ne mai matukar muhimmanci a jikin ‘ya mace domin shine cikon matantakarta koh a cikin ‘yan uwanta mata bare a wurin mijinta da bashi da shi dole ne mace ta kula dashi sosai.

Akwai nonuwa masu shape da dama koh a nan sai mace ta kula da kalar brazier da zata rinka amfani dashi.

  1. Akwai mango shape shine wanda nipples din su ke kallon sama irin wannan nonon baya saurin zubewa da wuri gaskiya zakiga koh haihuwa nawa mace tayi nononta bazai zubeba.
  2. Sannan akwai pointed breast (shine wanda zaku ga yana kallon gaba (straight) gaskiya irin wannan nonon yana saurin Zubewa da wuri sai ana gyarashi sosai.
  3. Akwai kuma nono mai kallon gefe zaku ga akwai gab sosai tsakanin nonuwan guda biyu, nonuwan zakiga harsu kusa shiga hammata, irin wannan nonuwan ma yakan Dan kwana 2 bai zube ba mai irin wannan nonon ta rinka amfanin da (bra) ta dinke distance between 2 curves na (brazeeya) din masu sauran shapes zasu amfani da normal straight (brazier) ba a son mace ta rinka amfani da (bra) din da ta matse mata nonon saboda zai rinka danne glanda kuma glanda din nononta zaiyi laushi ta yanda dole ne nononta ya fadi sai mu kula domin nono adon ‘ya mace ce.
  4. Sannan akwai nono wanda hausawa suke kece mishi mai gindin tasa, shi zaki ganshi baida tsawo sosai amma yana da fadi in (Allah) ya azurta mace da irin wannan nonon zaki ga koda ta haihu ne baya zubewa, wannan ya kamata ta kula dashi sosai don kuwa ba karamar kyauta Allah yayi mata ba gaskiya.
  5. Sannan inason maza kusani idan akace mallakar miji bayana nuna cewa mata kawai ke da wannan gyaran ba.
  6. Sannan kuma mata bafa koh wanne namiji bane yake son manyan nonuwa ba.
  7. Haka kuma ba koh wanni namiji bane yakeson kananan nonuwa ba.

Duk yanda Allah yabaki toh barshi a haka saidai gyara da zaki rinka yin mishi.

Mata don Allah ku dinga gyaran nonuwanku domin Sune ku, sannan Sune ke daukar hankalin maza.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.

Apply Now

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button