Hanyoyin Da Suke Haifar Da Gautsin Fata:
Assalamu Alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu Mai albarka na arewamusix.com
Akwai abubuwa da dama da sanyi ke janyo wa fata, kamar gautsin fata da sauransu, a saboda hakane yau na kawo muku yanda wadannan al’amura ke faruwa da kuma yanda zaku magance su.
Ku sani cewa fata itace mace, in ta yi kyau za ta rika haskawa a lokacin tashen shekarunta, in kuwa ta baci lallai tsufan mace zai bayyana da wuri, koh da ba ta kai shekarun ba don haka saimu kula da fatarmu.
Rashin shan isashen ruwa a Jiki: shi ruwa na da matukar mahimmanci a fata, don haka ya kamata a dage da shan ruwa da kuma cin kayan lambu wato kayan marmari da kuma ’ya’yan itatuwa, rashin shan ruwa na haifar da gautsin fata sosai.
Yin amfani da sabulu mai zafi, yawan amfani da sabulan dake dauke da sinadarai masu karfi na illatar da fata da kuma haifar da samun gautsi a fata, don haka sai ku kula, ki samu sabulu wanda ba su dauke da sinadaren illatar da fata kamar su sabulan yara da sauransu.
Kura, shima kura yana karya sinadarin bitamin a jiki wanda ke da mahimmanci wajen gyaran mataccen fata, sannan a rage bude fatar jiki a wajen da yake da kura, domin ba iskar gari kawai ke kawo shi ba, shan taba sigari koh kuma zama a inda ake sha zai iya zama matsala ga lafiyar fatan.
Shafe-shafe: sannan yawan amfani da kayan shafe-shafe da ake yinsu da sinadaran maiko na shanye maikon dake cikin fata, kuma hakan yakan haifar da yamutsewar fata sosai.
Yin amfani da mayuka masu dauke da turaruka masu karfi: matsalar dake tattare da amfani da irin wadannan mayukan sune, yawan shafa ta a lokuta da dama, na sanya sinadaran dake gyara fata ya daina amfani a jikin mutum.
Gyaran gaba wato (farji) ga uwar gida da kuma mata masu fafakakken gaba shine (Matsi).
Ana son uwar gida ta kula da gabanta musamman ga wacce tayi sabon haihuwa in kika bari gabanki (farji) ya lalace toh kamar zubar da kimarki ne a wajen mai gida, yake uwar gida kada ki barshi yayi wari, kada ki barshi yayi fadi, domin masana ilimin kiwon lafiya da jima’i sunce duk lokacin da aka yi jima’i da mace farjin ta yana kara fadi shi kuma azzakarin mai gida yana rage girmane toh kuwa kinga nasa na rage girma naki kuma yana kara fadi, rashin kula da kuma neman mafita a hakan yakesaka maza da dama suke ganin matayensu a matsayin tsofaffi ta bangaren jima’i, wanda hakan kuma kema uwar-gida rashin kula daga wajen maigidan naki takansa kema ba kya jin gamsuwa sosai a duk lokacin da kuka gabatar da ibadan aure wato (jima’i) don haka sai ya fara tunanin kin tsufa ke ma ki fara ganin yazama rago, kuma ba kowane namiji bane zai iya fadawa matarsa gabanta ya kara girma ba, hakama Kuma ba kowace mace bace zata iya gayawa maigidanta rashin gamsuwar ta ba, don haka uwargida da maigida sai a kula.
Ga Wannan hadin Gareki Uwar Gida:
- Farar albasa
- Kanunfari
- Citta
- Balmo
- Barkono
- Rihatul hulbi
Zaki hadesu duka a waje daya ki mayar dasu kamar yaji kina zubawa cikin abinci kina ci kullum, toh in shaa Allahu uwargida da maigida zakusha mamaki, domin kuwa gabanki zai cike yayi cif-cif kuma zaki dawo tamkar sabuwar budurwa ga maigidanki in shaa Allah.
Bayan haka kuma, zaki iya samun zogale mai kyau amma danyen ganyen, ki wanke sosai, kisa a Blender, ki markade shi, har sai yayi laushi, har ki ga yana yauki, sannan ki tace shi sosai, bayan kin tace ruwan, sai kuma ki nemo madarar gwangwani na ruwa, misali irin madarar peak (na ruwa), ki juye a ciki, ki dan saka zuma Kadan ba da yawa ba haka zaki rinka sha a kai a kai.
Ga Hadin Maigida Shima:
- Murucci
- Saiwar haukufa
- Namijin goro
- Hanno
- Rihatul hubbi
Zaki hadesu duka, saiki daka su gaba daya, ya dinga zubawa a nono mai kyau yana sha, sannan ku nemi dabino ku daka shi ya sa a cikin nono mai tsami sai ya rika kama ruwa da shi, amma fa bayan ya gama shafawa zai iya wanke wa da ruwa.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.