Yanda Zaki Gyara Nononki Kafin Kiyi Yaye Da Kuma Bayan Kinyi Yaye Da Zubewar Nono Tare Kuma Da Hadin Gyaran Fata Da Gashi

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a Wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku a wannan shafi namu Mai albarka na arewamusix.com
Shi nono babbar kadara ne kuma kyawunsu yana kara miki kyau da kima gurin mijinki, idan kuma sun lalace toh zakiji kema da kanki baki son ganinsu balle Kuma akaiga mijinki, saboda haka dole ne ki dinga kula dasu yanda Yakamata, akwai hanyoyi da dama na kula da lafiyar nono, ga wasu kadan daga cikinsu:
Yanda Zaki Kara Girmansu Da Kuma Hanasu Zubewa
Zaki Samu:
- Farar shinkafa
- Garin Alkama
- Garin habbatus sauda
- Garin Ayaba (Plantain).
- Gyada mai malfa (mai zabo)
- Aya Madarar gari.
- Zuma
Dafarko zaki bare bayan plantain sai ki yanka shi, ki shanya ya bushe, sai ki daka, ki hada da garin alkama da garin farar shinkafa, sannan ki hada aya da gyadar a markada a tace ruwan, bayan haka sai ki dorashi a kan wuta ki zuba garin Plantain da alkama da farar shinkafar da muka hadesu a guri daya, sai kuma ki zuba garin madara da zuma, ki damashi yayi kauri sosai, saiki rinka sha safe da yamma. Idan kina shirin yin yaye ne, toh ki shashi sati biyu kafin yaye, in kuma ba kya shayarwa, za ki iya sha, sai ki tanadi rigar nono, wato Brazier mai kyau, wanda zai rika tallafawa nononki su tsaya sosai, ki rika sakawa wanda ya matseki wato yayi (tighten) dinki.
Kiyi wannan hadin na tsawon sati biyu in shaa Allahu Zaki samu abinda kikeso gameda nononki.
Idan kuma baki da halin siyan duka wadannan kayayyakin saboda halin rayuwa da muke ciki, toh kina iya yin kunun alkama ki rinka sha sau 2 a rana, amma za ki rinka sa madarar gari, wato kunun alkama da madara ke nan.
Koh kuma ki samu garin hulba, ki tafasashi ki rinka gasa nononki dashi, sai kuma ki rinka shafa man hulban a kan nonon zakiga abin mamaki sannan kuma idan kin samu Kwan salwa ki fasa ki rinka shafawa a nonon, kuma ki fasa guda 3 kisha su a danyensu.
Sannan ki samu waken soya ki cire dattin ki sa a wuta kidan soyashi sama-sama ammafa karki sa mai hakanan zaki saka shi cikin tukunyar zakiji yana kamshi toh saiki sauke idan yasha iska kidaka yayi gari saiki samu ridi shima ki soya sama-sama ki daka yayi gari toh ‘yar’uwa kullum da safe ki diba wannan garin waken soya ki zuba a cikin ruwan zafi ki shanye sannan ki samu kunun aya mai kyau ki zuba garin ridi ki dinga sha sau 3 a rana,
Yanda Ake Amfani Da Ganyen Shayi Domin Gyaran Fata
Ganyen shayi yana da amfani a jikinmu sosai, domin shan sa na kara lafiya da kuma rage gautsin fata musamman a wannan lokacin da muka shiga na hunturu, kowane ganyen shayi yana da nasa amfanin a jiki amma koren ganyen yafi muhimmanci.
Zaki iya shafa ganyen shayin a fuska, koren ganyen shayi yana kare fata daga saurin tsufa.
Kuma yana kare jikinmu daga cututtuka da dama. Yawan shan koren ganyen shayi na sanyawa a ga mutum kamar saurayi, nan kuwa yanada shekaru.
Yanda Zaki Hada Man Da Zai Gyara Miki Gashi, Laushi Hadi Da Tsantsi
Abubuwan Bukata:
- man dalbejiya
- man kade
- man madaci
- man zaitun
- man kanumfari
- man gyada
- icen dogon yaro
- icen sandal
Zaki samu mangyadanki ki daura a kan wuta kisa dogon yaro da sandal ki barshi ya tafasu sai ki juye sauran maya-mayan ki barshi ya nuna sai ki sauke ki barshi ya huce kisa madaran turare, saiki samu robarki Mai kyau ki zuba a ciki, idan kikai wannan hadin zaki sha mamaki in shaa Allah.
Share domin wasu su amfana.