Illolin Dake Tattare Dayin Bleaching Ga Mata Da Maza:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na arewamusix.com
Akwai wasu abubuwa guda biyar da zan kawo muku yanzu wanda suke illah ne ga masuyin bleaching.
Abubuwan Kuwa Sune:
- Canzawar kalar fata, fata ta zama kala daban-daban.
- Ciwon daji na fata.
- Sai cutar mantuwa.
- Sannan ciwon koda.
- Ciwon hawan Jini.
Ana kallon mai yin bleaching da abubuwa guda biyar
- Nuna gazawa ga Allah ta’ala
- Sannan mai kushe halittar Allah
- Kuma mara godiya ga Allah subhanahu wata’ala
- Abin Ƙyama ga al’umma
- Kazamiya koh kuma kazami.
Don Allah Duk wanda ya karanta yaturawa ‘yan uwa koh hakan zai zama sanadin da masu yin bleaching zasu daina yin bleaching din gaba daya.
Allah ya karemu da karewarsa, ya rabamu da aikata duk Wani aikin dana sani, ya rabamu da sauya launin fatarmu, dama makamancin abinda ba addini bane yazo mana dashi ba.
Yaa ubangiji karabamu da rudin duniya da zamani, da sharrin shedan aamin yaa hayyu yaa qayyum.
Wa’inda sukeyi Kuma Allah yasa su gane su daina su dawo hanya madaidaiciya albarkacin fiyayyan halitta Annabi Muhammadu (S A W) aamin yaa hayyu yaa qayyum.