Abubuwan Da Zakiyi Wanda Zaisa Ki Dauwama Cikin Zuciyar Mijinki/Masoyinki:
Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu Mai albarka na arewamusix.com
- ‘Yar uwa ki rinka yi masa halin mata, wato irinsu kisisina, shagwaba da sauransu, don namiji baya son mai halin maza ta zama matarsa gaskiya.
- Sannan ki zamo mai iya kwalliya, idan kin kasance mai zaman gida ce toh kici ado koh da kuwa bazaki fita koh zuwa koh ina ba toh kiyi kwalliya.
- Sannan kada ki fara lissafowa mijinki matsalolinki koh na gida a lokacin daya shigo, ki barshi ya huta tukunna ya samu nutsuwa sannan saiki fada.
- Ki zamo mai kirki, ladabi da biyayya ga mahaifiyar mijinki kamar yadda zaki so shima ya zamo kamar haka ga mahaifiyarki.
- Har ila yau ki dinga karawa mijinki karfin gwuiwa akan abinda kika ga alamar yana nema ya karaya, hakan zai sa yazama gwarzo a cikin maza.
- Ki dinga fadawa mijinki cewa kina sonshi sau dayawa, dayawa dayawa, Aisha radhiyallahu anha tace Annabin tsira SAW ya kasance yana tambayarta ya karfin soyayyarta a gareshi, sai tace mishi kamar ‘zarge’ (wato dauri ko kulli wanta bazai kwance ba), sai ya sake tambayarta ‘shin yaya zargen yake’? Kuma ya kasance yana cewa da ita Allah ya saka miki da alkhairi Aisha, ina farin ciki da jin dadi dake fiye da yanda kike farin ciki dani.
- Ki dinga yawan sada zumunci ga mutanen gidansu (kamar ziyartarsu, kiransu a waya da dai sauransu).
- Sannan ki dinga bashi wani dan karamin aiki a gida kuma idan yayi aikin sai ki gode masa, hakan zaisa ya kara dagewa akan wanda yakeyi.
- Ki dinga karfafa mishi zuciya wajen yin aikin alkhairi.
- Idan yana cikin damuwa ki dan bashi lokaci, da yardar Allah sai kiga ya dawo dai-dai kamar da.
- Ki dinga yin masa godiya akan sama miki abinci da muhalli da yake yi, abune mai girma gaskiya.
- Ki rinka tuna cewa mijinki ma yana da damuwa da farin ciki, saboda haka ki dinga tunawa dashi wajen yanke hukunci.
- Sannan idan mijinki ya nuna damuwa akan dan karamin abu da kika yi masa toh saiki bashi hakuri kuma kice kin daina.
- Kiyi dukkan abubuwan da aka lissafo saboda Allah, sai kiga Allah yasa miki albarka a cikin duk abinda kike yi, Allah ya kawo mana albarka da yalwatar arziki data ‘ya’ya a cikin rayuwar Aurenmu. Aamin
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.