Yanda Zaki Hada Magi Da Kanki A Cikin Gidanki Harna Siyarwa Zaki Iya Hadawa:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu Mai albarka na arewamusix.com

‘Yan uwa a yau na kawo muku yanda zakuyi hadin magi dakanku Kuma a cikin gidanku cikin sauki.

Abubuwan Dazaki Bukata:

  • Waken soya 6 cups
  • Gishiri (salt) 6 cups
  • Ajino moto 3 cups
  • Suga 3 cups.
  • Garin citta
  • Garin masoro
  • Garin Tafarnuwa
  • Kaninfari dan kadan akeso
  • Nutmeg
  • Dan tsami
  • Garin albasa koh kuma garin lawashi (3 tablespoon)
  • Kimba (optional)
  • Food color (brown)
  1. Zaki Samu tukunya ki zuba waken suya ki daura shi akan wuta kina soyawa a hankali har sai ya fara canza kala kinga harya fara tsagewa.
  2. Sai ki dauke ki barshi ya huce sannan ki bayar akai Miki nika, bayan an kawo miki nikan sai ki Kara mai dashi kan wuta kinayi kina juyawa saboda kar ya kone har sai ya canza color ya fara kamshi, dan indai bai soyuba zakiji in kinyi maggin bazaiyi miki dadi ba gaskiya, zai dinga taste kamar garin waken suyane, sai ki sauke ki ajiye shi a gefe.
  3. Bayan nan sai ki dauko gishirin ki, ki tankade shi ki kawo ajino moto dinki, da Dan tsami kamar half teaspoon, sai ki dauko sugar ki hada ki nikasu koh a blender ne haka, amma ba da gishirin zaki hada ki nika ba sai kin nikasu zaki dauko gishirin ki hada dasu.
  4. Bayan nan saiki dauko garin albasa ki zuba, ki dauko kayan kamshinki ki hada su guri daya ki auni cokali biyu shima ki zuba a cikin wannan gishirin da Kika hada da ajino moto da sugar da dan tsami.
  5. Sannan saiki hada su guri daya gabaki dayansu da garin waken suyan da hadin gishirin kiyi ta juyawa har sai ya hade jikin shi.
  6. Idan ya gama hade jikinshi sai ki sami food color dinki preferably ki samu na gari sai ki zuba shi a cikin ruwa, amma ruwan kar ya wuce rabin Kofi, sai ki dauko wancan hadin garin naki ki dinga yayyafawa aciki kina yi kina juyawa zakiga yana canza color har sai kalan ya canza gaba daya.

Shikenan sai ki baza a faranti yasha iska idan yasha iska sai kiyi packaging dinshi, in kuma so kike yayi cube irin yarda magi yake zuwa zaki kara ruwa ne maimakon rabin Kofi da zakisa sai ki saka ya danfi haka yanda kina zuba ruwan yana hade jikin shi har sai yayi tauri sai ki samu wannan abin ice cube dinnan na freezer ki saka shi aciki ki saka a freezer for like 8 hours zakiga ya kankare sai ki banbare ki zuba shi a mazubi, shikenan kin gama.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.

Apply Now

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button