Wasu Dabi’u Goma Sha Hudu Da Mace Mai Aji Da Kamun Kai Ta Siffanta Dasu:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu Mai albarka na arewamusix.com

Ga siffofin da za’a gane mace mai aji da kuma kamun kai.

Itace macen da tasan darajar kanta da kuma addininta ta hanyar gujema duk abinda zai taba mutum cinta.

Sannan kuma itace macen da bata shiga abinda babu ruwanta domin gudun kar arainata.

Haka zalika itace a koda yaushe take suturta jikinta domin tana matukar kishin kanta.

Har ila yau itace wanda bata tara samari koh kuma kawaye barkatai saboda gujema kananun maganganu koh kuma a wulakanta ta.

Itace macen da bata daukan raini don ba ta raina kowa itama bataso a rainata.

Kuma itace wanda bakajin hayaniyar ta a inda ake yawaita surutu don tafi kowa kishin muryanta.

Har ila yau dai itace wanda bata saka hotunanta a social media saboda tana matukar tsoron abinda zaisa aga surarta da abinda zaije ya dawo.

Itace mace mai girmama duk wanda ya girmamata don tasan darajar su koda akwai wa’inda basa sonta.

Sannan itace komin sanda takema namiji bata bari har yaga fuskar da zaiyi wasa da sasan jikinta.

Idan akace mace mai aji kana iya samun soyayyarta ammafa ba a cikin sauki bane zata iya bari ka shawo kanta.

Ita mace mai aji takan koma mara aji a lokacin da take matukar sonka hakan nafaruwane saboda tunaninta kaine zaka aureta.

Kuma itace mace mai qualityn da kowani namiji yake mafarkin ganin ya aureta ta zama uwar ‘ya’yanshi.

Akwai banbanci tsakanin jan aji da kuma girman kai da mace keyi amma saika sa hankali gami da tsaida tunnaninka waje daya sanan ka nazarta hakan.

Yake ‘yar uwa ki kasance mace mai aji koda kuwa mutane zasuyi ta sukarki da bakaken maganganu akanki hakan shawarace kyauta na baki.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.

Apply Now

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button