Yanda Zaku Magance Bushewar Lebe Musamman Lokacin Sanyi Nan (DRY/CHAPPED LIPS)
Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi Mai albarka na arewamusix.com
A yau in shaa Allahu zanyi muku bayanine dangane da leben baki yanda za’a kula dashi especially a wannan yanayi da muke ciki na sanyi wato hunturu.
Shi bushewar fatar lebe yafi samuwa ne a cikin lokacin sanyin Nan da muke ciki, amma ga mafi yawan mutane, wasu kuma ta dalilin allergies, wato yawan shiga rana, koh yawan lasan lebe, koh rashin ruwa a jiki, koh kuma rashin shafa mai abakin da wasu lalurori najiki.
Hanyoyin Da Za’abi A Maganceshi Kuwa Sune:
- Baking powder: Shi yin amfani da baking soda/powder amatsayin chemical exfoliant yana taimakawa sosai wajen dago da busheshe da matacciyar fata a hankali batare da bareshi da karfi dayaji ba, ba kamar yin amfani da misali sugar da ruwa ba wajen exfoliating leben ba.
Yanda ake amfani dashi ku shine: Za’a diba kadan da yatsu biyu a zuba adan kwano, sannan a diga mishi ruwa kadan sai a juya, sai a rinka ashafa a leben, abarshi yayi akalla na sekonni 30 sai awanke leben da ruwa, a samu kyalle mai kyau adan dirje leben amma bada karfi sosai ba, sannan a shafa man baki (lip balm), a rinka yin haka kullum tun balle bayan angama wanka.
Amma Wasu Hanyoyin Sun Hadane da:
- Yin amfani da man lebe akai-akai
- Shan isasshen ruwa
- Yin amfani da humidifier adaki
- Daina lashe lebe
- Daina bare busheshshen fatan lebe
- Daina amfani da mayukan lebe masu menthol, camphor da eucalyptus saboda suna kara busar da lebene gakiya.
- Sai ganin likita idan har leben yacigaba da bushewa bayan bin ka’idojin sama saboda zai iya zama infection ne ko ciwon daji wato (cancer), Allah yayi mana tsari da Cutar cancer.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.