Wasu Daga Cikin Kura-kuran Da Mata Keyi Yayin Kwalliya Cikin Rashin Sani

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku a wannan shafi namu Mai albarka na arewamusix.com
Shi kwalliya idan baki tsaya kin nutsu kin gyara ba, sai kiga fuskar ki kota wanda kikayi mawa tayi kama da ta dodo.
Akwai kura-kurai da dama da mata keyi wajen yin kwalliya ba tare da sun San yin hakan kuskure ne ba.
Ya kamata duk wacce zatayi kwalliya ta kiyaye idan tazo shafa kayan kwalliya a fuskarta ko fuskar wanda kikewa musamman wajen sanya gazal da hodar fandeshon da janbaki da sauran kayan kwalliya wadanda ba su dace da kalar fatar mutum ba.
A yau na lissafo irin kurakuren da mata ke yi wajen kwalliya. Idan ba a gyarashi ba, sai a ga fuskar mutum ta zamo tamkar ta dodo.
YANDA ZAKUYI MAGANIN KAUSHIN KAFA KOH FASO CIKIN SAUKI ANAN
Shafa hodar fandeshon wanda bai dace da fatar mace ba:
Sau da yawa sai kiga mace ta yi kwalliya da hodar fandeshon da bai dace da launin fatarta ba.
Ya kamata idan Zaki kwalliya ki sami launin fandeshon wanda ya dace da launin fatar mace kafin kiyi amfani dashi.
Shafa kayan kwalliya a fuska mai gautsi:
Idan kika shafa kayan kwalliya a fuska ba tare da shafawa fuskar mai kadan ba, lallai kwalliyar baza ta yi kyau ba zakiga tayi mk wani busur-busur.
Man jiki ko na fuska na gyara fata saboda haka, ya kamata ana shafa man fuska kafin shafa hodar.
Idan kina da lebe manya bai kamata ki cika lebenki da gazal ba, domin yin hakan zai kara fitar da girman lebenki ne.
Toh amma idan ke mai kananan lebe ce zaki iya bin lebenki da gazal din baki (lip liner).
- Amfanin Gazal a gira: Idan ke mai cikakkiyar gira ce , bai kamata ki dada wata gazal a kan girarki ba idan kikayi hakan zakiga yayi yawa bazaiyi kyau ba.
Sai dai idan ke ba mai cikakkiyar gira ba ce, za ki iya cika girarki da gazal wanda kalarta ta yi dai-dai da gashin girarki.
- Idan Kuma zaki shafa hodar ‘blush’ toh ki tabbata cewa kina da farar fata domin wannan hodar tafi dacewa da mai farar fata wato fararen mata.
Ki tabbatar da cewa kin jagira dai-dai a kowane ido domin ba a son wata girar ta yi sama dayar kuma ta yi kasa yin hakan na bata kwalliyar mace sosai don zakiga girarki daya tafi daya yin sama Kinga koh kwalliyar tayi babu tsari.
Ayi share domin ‘yan uwa su amfana.