Yanda Akeyin Hadin Mallaka Na Musamman Ga Matan Sunnah
Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku a wannan shafi namu Mai albarka na arewamusix.com
Hadin Dake Gigita Mai Gida gida:
- Jan Apple
- Madara ta Gari sachets
- Zuma mai kyau wanda bayida hadi
Dafarko zaki bare apple din ki yayyan kashi kanana-kanana, sai ki samu mazubi mai kyau ki juye madarar gabadaya ki zuba zuma a ciki cokali uku, shi baa a sa mishi ruwa, idan babu zuma asa suga mai kwaya 3 cubes, sai a rinka sha sau 2 a rana har tsawon kwana 7.
Ga Wasu Hadin Musamman Ga Mata:
HADIN RIDI: Anason miji da mata su ringa amfani da wannan hadin domin Karin ni’ima yana kuma sa a koda yaushe ki dinga bukatar mijinki kusa dake.
GARIN RIDI: Zaki Samu kankana ki kasa kashi 3, saiki dauki kashi daya daga cikin ukun ki hadasu ki zuba a cikin blander ki markade, saiki zuba garin ridi a ciki, ki zuba madara da zuma ki zuba wa angonki cikin kofi kisha shima yasha wannan hadin yana kara ni’ima da maniyi, sannan kuma yana hana karnin dake fitowa.
Zaki Samu:
- Ruwan Kwakwa
- Madaran peak
- Zuma
- Ridi
Ki hadasu duka a waje daya ki rinka sha yana kara ni’ima sosai.
Ga Na Karin Ni’ima Da Kuzari anason miji da mata su rinka sha domin motso musu da sha’awarsu
Zaku Samu:
- Kaninfari
- Zuma
- Garin Ridi
- Nonon shanu mare tsami
Ki dafa kaninfari da ruwan zafi idan ya dauko nuna (dahuwa) sai ki sauke ki sami garin ridi da nonon shanu mara tsami, ki hadeau guri daya ki gauraye ki saka a firij koh ki saka kankara idan yayi sanyi saiki sha, wannan hadin idan kinyi sai kuma bayan mako daya zaku kuma yin Wani.
Hadin ‘Ya’yan Itatuwa Wanda Yake Kara Ruwan Gaba:
Wannan hadin yana kara ruwa sannan kuma mata da miji duk zasu iya yinshi susha .
- Kankana
- Kukumba
- Tumatur
- Mazarkwaila
- Madarar peak
- Dabino
Zaki yayyanka kankana duka harda ‘ya’yanta, itama cocumba dukkanta zaki yanka harda bayan kar ki cire ‘ya’yan, ki yanka tumatur shima kada ki matse ruwan cikin sa sai kidaka kaninfari ki jika dabino ki cire kwallayen ki hadesu guri daya, ki markada a blander sai ki juye ki saka mazarkwaila ta narke ki zuba zuma ki juye madara peak gwangani daya, ki rinka sha safe da yamma zaki sha mamaki matukar kikayi wannan hadin.
Hadin Kaninfari Don Motso Sha’awa:
Zaki jika kaninfari shi kadai ki rinka shanshi ki rinka kuma kama ruwa dashi wato (tsarki) shima wani nau’in Karin ni’ima ne.