Hanya Mafi Sauki Da Zaki Gane Lokacin Ovalution Period Dinki wato (Lokacin kyankyasar Kwayoyin Haihuwa)

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi Mai albarka na arewamusix.com

Yana da matukar kyau da kuma muhimmanci ace mace ta rike ranakun zuwan hailarta wato al’adarta kamar dai yadda wasu likitoci suka yi bayani akai.

A wasu lokutan da dama matsalar rashin haihuwa ga wadanda suka yi aure hakan yakan samo asali ne tun daga rashin fahimta akan al’amuran da suka sha bamban, da kuma suka shafi yadda halin da jikin mace yake ciki, wannan kuma har da Ovulation, wato lokacin da kwan haihuwar mace yake kyankyashewa.

Ovulation shine wani lokaci da mace ke fafe kwan haihuwarta wanda da zaran ta fafe idan ta kusanci namiji shikenan sai ciki yashige ta da ikon Allah.

Duka 48hrs ne kacal idan ya wuce sai wani watan amma wasu lokutan bisa ga hikimar Allah kwan yakan kwana biyu yana jiran abokin tafiyarsa wato kwan da namiji kenan, akwai ciwon mara slightly painless contraction ba menses kikeyi ba menstral pains ne, ciwon daga hagu ko dama, wani lokaci idan kinji duka side biyu din.

Lokacin ovulation lalle idan kina da kula zaki iya ganewa, mata don Allah mu dinga kula domin akwai wani irin painless contraction da zakiji, mun dai san fallopian tubes dinmu guda biyu hagu daya a dama. So duk wata daga gefe daya ne kwan zai fito.

Ga Wasu Kadan Daga Cikin Alamomin Ovalation:

  1. Na farko shine painless contraction zakiji wani irin ciwo a hagu ko dama na mararki.
  2. Sannan zaki dinga jin menstrual pains slightly amma ba menses kikeyiba.
  3. Areola wato black point na nononki zai kara baki kuma nipple dinki wato kan nononki zai mike yayi erect kuma zai rinka miki zafi kadan-kadan musamman idan ana tabawa.
  4. Vaginal fluid wato majina mai tsananin danko wanda yake zama kaman spring zai dinga fito miki a gabanki.
  5. Matsananciyar sha’awar namiji zai kama mace a wannan lokocin.
  6. Temperature na jikin mace zai karu sosai, jikin ta yana daukan zafi, kuma ba zazzabin rashin lafiya take ba.

Lokacin ovulation wani lokaci ne na musamman da ya kamata mu kiyaye idan kuma kayi rashin sa’ar mai gida baya gari kokuma ba kwananki bane toh lallai kinyi missing sai kuma wani watan idan ya zagayo, sai dai Kuma yana da matukar wahala gane hakan.

Idan Kina son Ki Gane Ovalution Period Dinki:

Ovulation: Yana faruwane a lokacin da mahaifa ta saki kwayayen halitta izuwa ga bututun haihuwa wato (Fallopian tubes) domin haduwa da sperm a samar da juna biyu.
Sannan ovulation yana faruwane bayan kwana goma sha hudu (14 days) a duk kwanaki 28 na period.
Har ila yau ovulation yana kasancewa ne idan hypothalamus wato wani bangare na kwa-kwalwa ya samar da gonadotropin release hormones to hanyar pituitary gland domin su samar da Follicle stimulating hormone (FSH) da Kuma Luteinizing Hormone (LH), su wadannan hormones din sune suke samar da kwayayen halittu bayan sun gamu da sperm a fallopian tubes toh daga nan kuma sai su wuce izuwa mahaifa bayan sati daya.
Toh idan ovulation ya faru kuma ba’a samu shigar sperm ba har izuwa sati biyu shine sai yabiyo period ya fita.
A wannan lokacin na Ovulation yana daga cikin lokacin da akafi saurin samun ciki wato juna biyu, hakan shine yasa ake bukatar kowacce macen tasan lokacin da take fara period din ta da Kuma lokacin da take gamawa domin hakan yana da muhimmaci sosai ga kowacce mace.

Kwayayen da ovulation yake tafe dasu basa wuce awa 12 hours zuwa 24 hours suke mutuwa, su ba kamar kwayayen sperm ba da yake kwanaki kafin ya mutu (12 to 24hours).

Yanda Zaki Gane Ovalution Period Dinki:

Da akwai hanyoyi da dama da mace zata gane tana ovulation daga cikinsu akwai:

  • Zuwan period
  • Hauhawar temperature
  • Majinar gaban mace
  • Calendar Method
  • Sai kuma amfani da Ovulation kit

Alamomin Ovalution sune:

  • Karuwar sha’awa
  • Kumburin breasts
  • Dan ciwon mara
  • Dan ciwon kugun
  • Kumburin jiki kadan
  • Hasken fata
  • Cervix dinki zai tsuke
  • Karuwar dan-dano/kamshi/wari
  • Karuwar Gani.
  • Canjawar Mode
  • Canjawar yanayin cin abinci
  • Zubar farin ruwa daga gaba

Kwanakin Da Akafi Samun Ciki Wato Juna Biyu Lokacin Ovalution:

Duk da cewa kwayoyin halittar mace suna mutuwane a 12 to 24 hours, shi kuma sperm din namiji yana iya rayuwa har izuwa kwana biyar kafin ya mutu, wannan yana nuni da cewa macen da take bukatar samun juna biyu toh zata iya kwanciya da namiji.

Wannan shine, Allah yasa mudace.

Ayi kokari ayi share wa sauran ‘yan uwa don suma su amfana.

Apply Now

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button