YADDA AKE DAHUWAR KAZA MEKYAUN GASKE
YADDA AKE DAHUWAR KAZA MEKYAUN GASKE
Ingredients
- Kaxa budurwa wadda Bata fara kwai ba
- Minannas
- Kantu
- Habbatussauda
- Kanunfari
- Seasoning
- Citta
Zaki wanke kaxarki sosae kisata tukunya kidake kayan qamshin dukkansu sannan kixubasu akan kaxar tare da seasoning dinnan da duk abinda kikeso domin dandano
Sannan kidorata akan wuta kidafa sosae ki dauki kantunki kidakashi sosae saeta dahu sannan kixuba akai
Inkinada man tafarnuwa da da hulba da habbatussauda da kanunfari da kantu duk xaki iya xubawa kiqara barinshi komae yaratsata sannan kisauke tanada kyau sosae da sosae