Hanyoyin Gyaran Fuska Wanda Bashida Illah Zaisa Kiyi Haske Kuma Yafitar Miki Da Tabbai Da Pimples:
Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu Mai albarka na arewamusix.com
Yanda Zaki Cire Tabon Fuskarki:
Dafarko zaki samu:
- Zuma
- Lemun tsami
- Bawon lemun zaki
Zaki daka bawo lemun zaki amma busasshe saiki zuba cokali biyu acikin zuma rabin gwangwani sannan saiki zuba lemun tsami guda daya saiki dinga shafawa kafin kishiga wanka da minti talatin.
Hanyoyi (10) Na Gyaran Jiki:
Har illah yauma na sake kawo muku hanyoyi goma wanda zakubi don gyaran jiki ba tare da kun kashe kudi a shagon kayan kwalliya ba, ya kamata mata su koyi dabaru da dama domin taimaka wa maigida, idan maigida ya saba ba da kudin sayan kayan kwalliya, toh ranar da babu kuma sai a hakura a gwada daya daga cikin ababen da muke kawo muku na gyaran jiki.
- Idan kina so ki gyara gashi toh zaki iya hada ayaba da kwai sai ki kwaba su sosai sannan ki shafa a gashi ki jira na tsawon mintuna goma sha biyar (15) zuwa minti talatin (30) sannan ki wanke.
- Domin gyaran farce Kuma, zaki iya tsoma hannunki a cikin man zaitun na tsawon mintuna biyar (5) sannan sai ki cire a kullum, zakiga farcenki yayi matukar kyau sosai.
- Ana amfani da zuma mai kyau domin samun fuska mai santsi da laushi, ana shafawa a fuska a jira na tsawon mintuna goma sha biyar (15) zuwa ashirin (20) sannan a wanke da ruwan dumi. A gwada wannan hadin sau daya ma a sati za a ga canji in shaa Allah.
- Sannan ana amfani da ruwan amfuna da ruwa ana wanke kai, yin hakan na cire dattin da ke makale a gefen gashin kai.
- Domin masu yawan shafe-shafe za su iya yanka lemon tsami biyu sai su rinka shafawa a inda yayi duhu, shi kuma yin hakan a kullum yana haskaka bakin da ya bayyana a wasu gabobi koh Wasu sassa nafata.
- Domin samun fatar jiki mai sulbi, zaki iya amfani da man zaitun da gishirin rafi ki kwaba saiki rinka dirzawa a fatar jiki a kalla sau uku a sati.
- Man kwa-kwa na matukar gyaran zubewar gashin kai, zaki iya shafa man kwa-kwa a fatar kai sannan ki shafa a jikin gashin, kibari ya jima ya Dade kamar na awa daya sannan ki wanke zakiga ikon Allah.
- Sai kuma maza masu son man gyaran gemu, zasu iya amfani da man kwa-kwa yanasa laushi, tsantsi hadida shekin gashin gemu.
- A samu lemon tsami sannan a zuba zuma a kai, sannan a rika shafawa a kan kurajen fuska, yin hakan na kashesu sosai kiga kin nemi kurajen kin rasa.
- Sannan man zaituun yana sanya santsin fata idan an kasance ana yawaita shafa shi a koda yaushe a matsayin man fata.
Don Allah ayi turawa sauran ‘yan uwa suma su amfana.
Hi friend,
I need your help with a problem I’m having with a young girl. She’s accusing me of disrespecting her, and unfortunately, it’s true. I made a mistake, but I really need your help to resolve this situation.
Can you please help me? I’m willing to pay for your assistance.
Please call me back as soon as possible at:
My whatsapp number: +17852192072
My phone: +16057866458
My email: jacobwhiteeagle@proton.me
Thanks,
Jacob