Abinda Yakamata Mai Ciki Tayi Lokacin Da Cikin Yakai Wata Tara (9) Da Kuma Lokacin Nakuda:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu Mai albarka na arewamusix.com

Abubuwan da mai ciki ya kamata ta fara yi idan cikinta ya shiga wata tara Lokacin da ya tsufa kenan, da abinda zatayi idan lokacin fara nakudanta yayi.

Tabbas mata da yawa sukan sha wahala sosai idan watan haihuwarsu ya kama domin Allah kadai ya san irin halin/yanayin da suke shiga., wannan shafin mai albarka, ya kawo maku wata fa’ida wacce tabbas mun tabbatar da ingancin ta idan aka jarabashi toh in shaa Allahu za’a dace duk wata mace mai shan wahalar nakuda toh ta samu zumanta mai kyau kaman cikin Kofi koh cokali ashirin da hudu ta shanyeshi anan take.

Abubuwan da mai Juna biyu ya kamata ta fara yi idan cikinta ya shiga wata 9 , da abinda zatayi idan ta fara nakuda shine.

Tabbas mata da yawa sukan sha wahala sosai idan watan ya kama domin Allah kadai ya san cikin irin yanayin da suke shiga, shiyasa wannan shafin mai albarka, ya kawo maku wata fa’ida wacce tabbas mun tabbatar da ingancin ta idan aka jaraba in sha Allah za a dace duk wata mace mai shan wahalar nakuda toh ta samu zumarta mai kyau kaman cikin Kofi koh cokali 24 ta shanyeshi a nan take.

Shi yasa yana da kyau sosai da zarar cikin mace ya kai wata 7 ta dinga tafasa ‘ya’yan hulba tana zama a ciki kullum sau daya in ya shiga wata 9 ta dinga yi safe da yamma, hakan yana taimakawa sosai wajen bude kofofin haihuwa kuma da wuya mace ta karu a lokacin haihuwar, sannan kuma mace zata samu garin hulba ta kwabashi da zuma ta dinga shan cokali biyu safe da yamma na cokali 2, tohfa in shaa Allahu za ta samu sauki sosai wajen haihuwa amma kada mace mai ciki tayi amfani da hulba har sai cikin ya tsufa ma’ana lokacin nakuda saboda hulba tana zubar da yaron ciki, tana saka mace tayi bari wato (miscarriage) a turance.

Allah yasa mudace don Allah duk wanda ya karanta posting dinnan toh yayi kokari ya turawa ‘yan uwa mata saboda a samu saukin nakuda sannan kuma a samu saukin fitar yaro daga cikin mahaifa Allah ya bada iko.

Apply Now

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button