Ga Wani Dan Tsokaci Game Da Mata Masu Juna Biyu:
Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu Mai albarka na arewamusix.com
Ayau Tsokaci Zanyi Akan Mata Masu Ciki:
Tabbas mata mutane ne dasuka cancanci girmamawa musamman macen da Allah ya azurta ta da tarbiya koh ince kamunkai koh kuma sanin yakamata.
Zaku yadda da maganata ne kadai idan kukaji irin matsalolin da iyayenmu mata suke fuskanta yayinda ciki yake kokarin shigansu, zakaji suna cewa, banga period dina ba, inajin ciwon kai, ga amai, ga tashin zuciya, ga kumburin nono, rashin karfin jiki, ciwon mara, zubar jini daga farji, karancin jini, bana samun isasshen bacci, ciwon baya, yin bayan gari mai tauri, ciwon Ƙirji toh duk wadannan wasune daga cikin alamomin shigan ciki ga mace, kina zuwa asibiti za’ayi miki gwaji dan a tabbatar miki, tabbas sai angwada akesanin gaskiyar lamarin.
Dazaran Ance Miki Kinada Ciki Toh Yadace Ace Kinada Wannan Ilimin:
Sanin kowanne cikin da bashida matsala yana daukan wata tara ne (wato sati arba’in kenan) kafin haihuwa, yakan iya kasancewa sati talatin da bakwai zuwa sati arba’in da biyu, toh abinda yakamata mukara sani shine malaman kiwon lafiya sun kasa lokutan zuwa gida 3.
Misali:
- Wata 3 na farko shi Ake kira da (FIRST TRIMESTER)
- Wata 3 na tsakiya shi ake kira da (SECOND TRIMESTER)
- Wata 3 na karshe kuma shi ake kira da (THIRD TRIMESTER)
Abin shine kowacce ga6a tanada irin canje-canje da maiciki zata fuskanta, canje-canjen basu wuce na sinadaran hormones (sinadaranda suke taimakawa kwayoyin halitta wato [cells] a turamce da tsokokin jiki wajen gudanarda aikinsu) dakuma na sassan jiki.
Sanin wadannan bayanin zaitaimaka muku wajen shiryawa tarban kowanni canji dazaku fuskanta, sannan zaku iya fahimtar abubuwanda zasu iya kasancewa ba ciki bane yake haddasasu, tahanyar gwaji a asibiti, iya adadin iliminki shine iya adadin jindadinki gameda ciki wato juna biyu.
Wata 3 Na Farko Wato (FIRST TRIMESTER):
Shi watan ukun farko yana farawane tun daga ranarda kika daina ganin period dinki wato (jinin al’ada), daukar ciki kuma zaifarane bayan sati biyu, wata ukun farko zai karene zuwa sati 12 da shigan ciki dukda cewa ta iya yiyuwa tagani da ido baza’a gane kinada ciki ba musamman a wata ukun farko, ammafa a lokacin jikinki zaikawo wasu canje-canje yayinda halittar dake cikin yake harhaduwa don yagirma, bayan yan satika da shigan ciki, level din hormones dinki zaiyi gagarumin canjawa, mahaifarki zaifara tallafawa igiyar mahaifa (wato placenta) da halittar dake cikinki dansu samu su girma, gudun jini zaikaru a jikinki saboda ta jinin iskar oxygen da sarrafaffen abinci da jikinki ya sarrafa yakebi ya isa zuwa halittar dake cikin, dan yaci gaba da rayuwa sannan ya girma, sannan kuma bugun zuciyarki zai karu, wadannan canje-canjen suna tafene da
Wadannan Alamomin:
- Rashin karfin jiki
- Ciwon jiki/kasala musamman dasafe
- Ciwon kai
- Yin bayan gari mai tauri
Wata ukun farko yanada matukatar mahimmanci da bunkasa halittar dake cikin mace, sassan jikinsu yana girmane a wadannan wata ukun farkon, tabbas lokacine mai muhimmanci, yanada kyau kikula da cin abinci masu kara lafiya gamida kara wani adadi na folic acid saboda kariya daga matsalar dazai iya shafan jijiyoyi masu isarda sakonni.
Shan tabar sigari, shan giya, dakuma shan magani batareda duban likita ba dabi’une masu hatsari ga mace maiciki harma da matsala wajen haihuwa, karki yarda kitsaya kusada maishansu (sigari), mata masu biyayya ga shawarwarin likitoti sunfi samun haihuwa cikin koshin lafiya.
A wata ukun farko akesamun barazanar yin 6ari, toh amma idan kina shan magangunan damasu ciki sukesha (vitamins) sannan kina kauracewa shan miyagun abubuwa toh tabbas kina bawa halittar dake cikinki gudummawa sosai akan lafiya dakuma tserancewa 6arin ciki, kaffen (caffeine) da soyayye koh dafaffen nama da ake sayarwa atasha bashida inganci gamai ciki musamman a watanni ukun farko, yakamata kikasance mai neman shawarwari daga likita akan irin abinci daya dace dake, yin hakan zai inganta lafiyarki dakuma jaririn dake cikin ki.
Wata 3 Na Tsakiya Wato (SECOND TRIMESTER)
Su watanni uku na tsakiya suna farawane daga satuttuka na goma sha uku zuwa ashirin da shida ga mafi yawan mata masu juna biyu, a wannan lokacinne yawancin alamomin ciki suke bacewa zaki iya samun karuwan kwarin jiki dakuma bacci mai dadi a dare dama yini.
Cikinki zaifara bayyana cewa kinada ciki yayinda mahaifarki yake girma daga lokaci zuwa lokaci, toh a lokacinne dazaki zuba jarinki a maternity wear, zaki kauracewa matsatstsun kaya sai dai ki rinka sa wadanda zasu sake Miki a jiki.
Bayan alamomin watannin ukun farko sun 6ace zakisake gamuwa dawasu alamomin kamar su kumburi koh kamewar kafafu dakuma zafi, kirjinki ya rinka kuna, zaki iya samun rashin jin dadin baki kuma nauyinki zayyita karuwa, wanda motsa jikinki dakuma cin hadaddun abinci masu gina jiki yana taka rawan gani akan karuwar nauyinki, jijiyoyinki, ciwon baya da yoyon hanci zasu iya bayyana agareki.
Watanni ukun tsakiya lokacine dazaki fara jin motsin halittar dake cikinki, amma mafi yawanci acikin satuka na ashirin, wasu suna cewa alokacin har sautin dayake tashi daga waje, halittar dake cikinki zai iya ji, za’a iya yimiki wasu screening saboda haka kiyi kokari wajen fadawa likitanki wasu abubuwa dasuka shafi kwayoyin halittar gadonki (family or genetic issues) dan likita ya tantance miki wadanda ka iya shafan jaririnki, toh a wannan gaban yanada kyau ayi scanning dan ganin koh lura akan shin ga66an halittar dake cikinki suna cikin koshin lafiya? Koh kuma a’a
Sassan Da Ake Dubawa sune:
- Zuciya
- Huhu
- Qoda
- Dakuma Kwalkwalwa
Haka zalika zaki bugaci ayimiki gwajin siga yayin da kike da juna biyu (gestational diabetes), sai dai kuma idan dama kina dashi koh kuma akwai mai gestational diabetes a danginku, tohfa yakamata ayi miki gwajin tunda wuri ( basai a wannan ga6arba), likita zai bukaci ki yawaita amfanida abinci masu daukeda sinadarin sugar/glucose saboda agane shin jikinki yana iya sarrafa siga yanda yadace koh kuma a’a?
Wata 3 Na Karshe Wato (THIRD TRIMESTER):
Su watanni ukun karshe sune daga satuka ashirin da takwas har zuwa haihuwa, awadannan watanni ukun karshen zaki kasance mai yawaita ziyartar malaman kiwon lafiya.
Ma’akatan kiwon lafiya zasu tabbatar anyi miki gwaje-gwaje kamar haka dan samar miki da ingantacciyar lafiya kafin lokacin haihuwarki
- Gwajin fitsari
- Gwajin hawan jini
- Sauraron bugun zuciyar halittar dake cikinki
- Awun girman ciki
- Duba hannaye da kafafuwa dan ganin shin sun kumbura?
- Gwajin adadin jini
Amma a wasu wurare gwaje gwajen yinafin haka koh kuma baikai hakan ba.
Zasu duba yanayin kwanciyar halittar dake cikinki wato jaririn dake cikinki sannan kuma suyi duba yi zuwa kusada mahaifa (cervix) dan nazari akan yanda jikin yake shiryawa haihuwar.
Amma a wasu wureren kuma, yayinda cikinki yakai satuttuka talatin da shida zuwa talatin da bakwai, sukanyiwa maicikin gwajin kwayan cuta maisuna group B streptococcus (GBS or Group B strep).
Itadin wata kwayar cutar bakteriya ce datake haifarda babban matsala yayin haihuwa, shiyasa za’a dauki sample din wani ruwa mai kauri daka farjinki zuwa dakin gwaji. Idan akayi sa’a baki daukeda GBS shikenan. Idan kuma akayi rashin sa’a kinadashi sai ayi gaggawar baki maganguna dan akashesu, tahakanne dake da jaririnki zaku samu kariya daga Group B strep.
Bayani akan ciki yanada matukar yawan gaske saidai mutum yayi tsakoci akai, Amma zamu rinka kawo muku lokaci zuwa lokaci in shaa Allah, sannan kuma daki-daki hakan zaifi saboda wani lokacin karanta rubutunma sai ahankali.
Allah ya saukeku lafiya masu juna biyu.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa suma su amfana.