Yanda Zaku Gane Banbancin Dake Tsakanin Matsi Da Kuma Cikowar Gaba

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu Mai albarka na arewamusix.com

  • Ga wani Dan bayani dazanyi muku, ida har ya kasance baki iya jin kina a matse dan yatsan da farji toh za iya zama kina da babban farji, sannan bugu da Æ™ari, idan kika saka yatsu 2 ko 3, misali manuninki koh kuma yatsan tsakiyar hannnunki (wanda yafi tsawo) a hakan kuma baki ji wani alamar bangon farjinki yana matse yatsun naki ba toh kina da buddden farji.
  • Amma idan ya zamanto kuma yana da wuya kamin kiji Æ™ololuwar dadi (orgasm) wato kawowa lokacin jima’i hakan na iya yiwuwa kina da budadden gaba ne Shima, haka kuma, raguwar jin dadi ba kamar daba shima duk yana iya zama alamar budadden farji ne.
  • Idan Kuma ya zamanto mace tana wasa da gabanta domin biyan buÆ™atar kanta, kuma tafi sha’awar ta saka wani babban abu a gabanta akan Æ™arami ma’ana bata jin dadin Æ™aramin abu idan ta saka a farji sai babba toh shima alamace ta cewa mace nada girman farji, Kuma yin hakan bayida kyau, don Allah mata ku kiyaye yin hakan.
  • Sannan kuma idan ya zamanto kina shan wahala kafin ki gamsar da mai gidanki wajen jima’i ba kamar daba.
  • Ko kuma ian ya kasance sai kin matse ko haÉ—e cinyoyin ki biyu sosai sannan kike jin dadin jima’i da maigidanki, toh wannan ma yana iya zama alamar budadden gaba gareki duk dai da cewa wani lokacin yana iya zamantowa mijin ne keda Æ™aramar al’aura. Amma idan kamin haihuwarki babu wannan matsalar sai daga baya to sai ki zargi budewar gabanki gaskiya.
  • Idan Kuma ya kasance kina jin Æ™arar fitar iska daga farjinki lokacin da maigidanki yake saduwa dake, iskan kamar fitar “tusa” amma ba tusa bace (fanny farting) kuma babu wari. Iskan yana shiga yana fitowa lokacinda maigida yake kaikawo, a fadarshi toh wannan alamace ta cewa kina da budadden farji.

Hanyoyin Da Zakibi Ki Tsuke Farjinki.

Da akwai hanyoyi da dama na matse farji musamman bayan haihuwa wanda sun hada da hanyoyin magani, motsa jiki (exercise), tiyatar likita domin rage girman farji da sauransu, wasu hanyoyin nada illah ga lafiya, wasu kuma hanyoyin basa da wata matsala koh hadari kamar dai yanda likitoci ke bayani akai

Ga Kadan Daga Cikin Hanyoyin:

  1. Motsa jiki , hanyoyin motsa jiki na zamani domin matse gaban mace suna da yawa (such as kegel exercises) da sunaye, motsa jikin ya shafi horo da mace zata iya bawa jikinta domin ya kasance tsokokin gabanta masu motsi sun kara Æ™arfi da tsukewa, misali, wata kwararriyar likita a India Dr. Sangeeta Gomes ( Consultant Obstetrician and Gynaecologist), ta bayyana cewa mace zata iya inganta tsukewar gabanta idan tana motsa jikin dauke numfashi (breathing exercises), zaki dauke numfashinki na tsawon ‘yan daÆ™iÆ™oÆ™i (seconds) kadan sannan ki tsuke farjinki na tsawon wani lokaci a lokacin da kike mai dauke numfashin, zakiyi hakan a kowace rana, sau 10 ko 15, sannan zaki iya yin hakan a kicin lokacinda kike aiki, a ofis, a tsaye ko a zaune , kohma a ina kuma a koh wani wuri ba tare da ma wani yasan abinda kike yi ba, sa’annan zaki yawaita cin ƳaÆ´an itatatuwa (kayan marmari) da abincin ganye (vegetables), wannan koh shakka babu zai taimakawa mace wajen matse gaba domin gyaran aurenta, wani nau’in motsa jikin kuma shine ake cema “Kegel exercise”. Yanda Dr. Gomes ta nuna cewa idan kina yin fitsari sai ki tsaida fitar fitsarin, wato ki riÆ™e fitarin, ki danne sa na tsawon daÆ™iÆ™oÆ™i 10 , wato ki Æ™irga 1 zuwa 10 sa’annan ki saki fitsarin a hankali a hankali, zaki iya yin hakan sau 2 ko 3 a rana idan za kiyi fitsari, shima wannan nau’in motsa jikin na tsuke gaban mace.
  2. Sai hanya ta biyu shine wanke gaba da ruwan sanyi mai Æ™ankara, Shima yana taimakawa wajen matse gaba amma sai an hada da motsa jikin da muka yi bayani, wannan yana daga cikin hanyoyin da Dr. Gomes ta zayyana. Amma zaifi dacewa ace sai mace ta gama wankan jegonta na kwana 40 kwata-kwata sannan tayi amfani da ruwan sanyin , wato bayan ta koma “normal”. SaÉ“anin yanda al’adar Bahaushe tayi imani dashi cewa ruwan sanyi na lalata gaban mace ,wasu likitocin a wasu al’adun na ganin yana matse gaban mace.
  3. Sai kuma yin amfani da alif (alum), shi alif yana matse gaban mace sosai sai dai likitoci na tsoratarwa akan yin amfani dashi saboda da sinadarin kemikal ne a cikinshi.
  4. Sai yin tiyatar likita domin rage budewar farji, wannan ma hanya ce ta zamani amma ana tsoratarwa akan yinsa saboda wasu dalilan lafiya.
  5. Yin yinÆ™urin tsuke gaba a lokacin saduwa, wato ki matse farjinki ta ciki lokacinda mijinki yake kaikawo, zaki yawaita yinÆ™uri domin tsuke gabanki hakan zaisa mijinki yaji alamun ana riÆ™e masa al’aura tamkar zobe ya zagaye gabansa, idan mace na yawaita yin haka toh zai zama É—abi’arta kenan kuma nan gaba ba zata san ma tanayin hakan ba saboda ta riga ta horar da jikinta hakan, kuma hakan zai inganta jin daÉ—in mijinta sosai, Allah ya taimaka yakara mana zaman lafiya muda mazajenmu.

Abubuwan Da Suke Ciko Da Naman Farjin Mace:

Mace zata samu kuma ya matse gabanta sannan yana saukar da ni’ima ta wani fanni kuma yana ciko da nonon mace.

Zaki Samu:

  • Nonon rakumi
  • Dabino
  • Kwakwa
  • Apple
  • Ayaba
  • Zuma
  • Man hulba

Yanda zaki hadashi da farko zaki tafasa nonon rakuminki kibarshi ya huce sai ki jika dabinonki ki cire kwallayen ki hada shi tare da apple saiki markada da Ayaba idan ya markadu saiki zuba zuma ki zuba man hulba ki juya shi sosai sai ki zuba a cikin fridge yadda ba zai lalace ba sai ki
rinka sha a kullum sai ki samu man hulba kina shafawa a gaban naki da nononki zaki sha mamaki sosai.

Don Allah kuyi sharing wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.

Apply Now

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button