Yanda Mace Zata Kula Da Jikinta Bayan Haihuwa:
Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu Mai albarka na arewamusix.com
Babban hatsarin da haihuwa ke zuwa dashi dake jawo asarar rayukan mata bayan haihuwa shine zubar da jini bayan haihuwa wato (Post Partum Hemorrhage) a likitance hakan na faruwa a stage na 3 na haihuwa, wannan shine lokacin da dariya ke rikidewa ya koma kuka, wato murna ya koma ciki, daga murnar haihuwa akoma kukan mutuwa.
- Sau tari wanda baisani ba zai iya tunanin fitar yaro shine haihuwa lafiya, wanda hakan ba shineba, wasu na ÆŠauka fitar yaro shine mafi mahimmanci, amma maganar gaskiya wannan bashine haihuwa lafiya ba, haihuwa lafiya shine aga bayan fitar yaro mahaifa ta murda ta harba wato contracton ta yadda hakan zai sanadiyar fitowar placenta wato ( uwa ta biya), kai wani lokacinma koda uwa ta biya akwai bukatar sai mahaifa tai wannan harbawar sannan idan bata harba ba hakan bazaisa jijiyoyin jini su toshe ba a saboda haka mace zata cigaba da zubar da jini, wanda wannan shine yike kashe mace, a wani lokacin ma hatsarin placenta din ce ma ke manne mahaifar ta yadda in aka jawota saidai ta taho hade da mahaifar ta tidota, shiyasa haihuwa tsallake siradi ce babba ba karami ba wallahi, muna adduar Allah yasa ‘ya’yayenmu suji kanmu, Allah yashirya mana zuri’a.
- Toh amma abinda yake taimakawa wannan harbawar shine ai maza-maza ai stimulating nonon mace, shiyasa wani lokacin ma in mace na naquda akan iya bukatar akawo yaron da take shayarwa domin ya kama nonon hakan yakan taimaka wajen samun contraction din mahaifarta, koh kuma inba yaro ace mijinta ya tsaya ya rika kama nononta, in kuma duka babu daya saide toh asamu nurses sui mata.
Shi wannan hikimar ta stimulating nipple yanada matukar mahimmanci har bayan haihuwa, wannan yasa game kallon finafinan likitoci na haihuwa zakuga da anciro yaro cikin jininsa da komi za’a dora ma uwa shi ya kama nono domin ya taimakamata wajen sa mahaifarta harbawa jinin haihuwa ya tsaya, shine hikimar skin to skin, nan da nan zakuga likitoci sun dorasa a nono, saboda hatsarin daka iya biyo baya, Allah yasa mudace.
Haka zalika wannan jinin haihuwar duk da anfi ganin zubarsa nan da nan bayan haihuwa cikin awa ashirin da hudu na yini, haka zalika kananun ma’aikatan lafiya kusani yana iya faruwa tun daga bayan kwana 1 da haihuwa zuwa sati 6 matukar Macen da akasan ta haihu kasa da sati 6 tazo asibiti da complaint na zubar jini toh kusani yana iya kasancewa Post Partum Hemorrhage ne har sai In kun gano wani abun na daban, don haka a lura dakyau, kar adau zubar jini matsayin ba serious abu ba don kurum kila anyi satuttuka da haihuwa ko kwana 3.
- Haka zalika koda baki fuskanci matsalar zubar jini ba ki daure ki shayar da babynki hakan zaici gaba da sa mahaifarki harbawa ta taso daga mararki ta koma kasan cikinki cikin sati 2 da haihuwa, hakan zai rage miki tsananin ciwon mara da duk da shayarwa akwai zafi wani lokacin.
- Bayan haihuwa ke diya mace kisani kazanta ba naki bane, baki daya tsaftarki dole ki nnkata fiye da da, walau C/s akai miki koh kuma normal da kanki kika haihu it does’nt matter.
Musamman tsaftar mara, matse-matsi zuwa farji kada kiyi wasa, saboda kinga a lokacin kina fitar da abinda muke kira Locia wanda ake kira jinin nifasi, wannan na dada saki vulnerable to infection. Sannan ki guji amfani da kayan matsi da sauransu kasa da sati 12 na haihuwarki, inma bazaki iya bari ba, kinki toh muna jiye miki tsoron endometritis ko sepsis. - Sannan kina iya yin wankanki koda aranda akai miki C/s ne, saidai ya zamto kina da akayan dressings duk sanda kikai wanka gurin ya jike ki zauna ki cire audugar, da bandeji din ki wanke gun da iodine ki canza sabon dressing din gun shikenan, inbaki da kayan yin hakan toh ki guji jiqa gurin ki rinka kebesa in kinzo yin wanka, sannan duk bayan kwana 3 zaki iya zuwa aduba koh kuma anemo ma’aikacin lafiyar da zai dubaki adai tabbatar gurin baya fidda ruwa inma yana ruwa toh atabbatar bame jini-jini bane, saboda gudun samuwar surgical site Infection da yana iya sa kwayoyin cuta sita cin fatarki a hankali a hankali suna qarawa gurin girma kizo ki shiga masifa, kilura da duk wani canji da zaki gani agun, karkiyi kasa agwuiwa kima likita waya ki fada mishi Koh kuma kije ki sameshi.
- Galibi bayan haihuwa cikin mata kan bude, zakiga akwai cin abinci, toh Hakan ba komai bazaisa ki nauyi fiye da kima ba muddin kina shayarwa, nauyin bazai canza daga yanda yake ba kafin ki samu ciki abaya.
- Bayan kwana 3 zuwa 5 da haihuwar galibi nono ke fara cika tsir-tsir ya rika ciwo, koda sha yaro yake yana zafi, don haka ba matsala bane ki rinka matsewa wani kaso saboda ki samu relief, kada duk sanda kikaji ciwo kice dole sai jariri yasha alhalin ya koshi, wannan kesa su yawan tumbudi, muddin kikaji jaririnki na gyetsa tare da yawan tsilla fitsara hakan alamace ta kyakkyawar shayarwa don haka in nono na miki ciwo dalilin cika saiki rinka matsewa kina ragesa.
- Wasu kanji ana cewa shayarwa na hana daukar ciki abunda ake kira lactation amenorrhea wanda hakan ke a amatsayin kamar hanyar planning, amma abunda bakusani ba shine sai macen dake shayar da yaro akalla duk bayan awa 4 zuwa 6 ce ke samun wannan benefit din, wato akai-akai akalla sau 6 zuwa 7 arana, sannan yakamata kusani hakan na tasiri ne kurum na tsawon watanni 6, wato adadin watannin Exclusive freeding, domin ga wacce ta cika watannin haihuwar cif ovulation dinta na dawowane bayan sati 6, wacce ta haifi bakwaini kuma ovulation dinta na dawo mata bayan sati 4, yayin da wacce tai bari kuma yakan dawo mata bayan sati 2, don haka daga wata 6 saidai ki za6i hanyar planning daban walau magani ko Kuma dai wata hanyar ta daban, inkinga baki samu ciki ba toh bakya ovulating kin taki lucky ne kurum. Amma maganin ma na plannin banda shan COMBINATION PILLS matukar kina shayarwa saboda zasu kawoma shayarwa matsala, zasu hindering milk production dalilin estrogen, saidai kiyi amfani da magani mai progestin kawai don haka kananun ma’aikatan lafiya fatan zaku kiyaye wannan.
- Ciwon nono ba bakon abu bane galibi saboda bacteria din da ake samansu asaman fata dakan shiga ta kafar nono koh ta nitsa cikin fata idan akwai karancin tsafta. Shyasa nake cewa ki gama ba yari nono kurum kija sale6ar bra din ki mayar, a’a ki samu tissue ko towel ki dangwali ruwa ki goge kan nonon sannan ki mayar, haka shima jaririn kinsa ruwa ki share masa nasa bakin.
Sannan idan kan nonon ya tsage muddin yana miki ciwo karki azabtar da kanki cewa dole sai kinba yaro ya kama ahakan, ki bashi dayan shi kuma mai tsaguwar ki rika matse ruwa daidai da wanda ake sha kina zubarwa, Is normal ne yin hakan.
- Koda babu tsaguwa abunda yake jawowa mace ciwon yayin shayarwa shine: dorawa jariri iya kan nono ya kama, indai zaki rinka dosana masa nipple dole kiji zafi, Areola wannan shatin duhun baki daya shine zaki tabbatar labbansa na tabawa, shi jariri bada lebe yake jawo nono ba shyasa macen dake shayarwa koda mijinta zaice zai kama nononta ya tsotsa saide taji zafi bazai ta6a iya zuqowa ba dan besan ya zaiyi ba yazo amma in jariri ya kama sai kaga har biyo kumatunsa yake, don haka ki samu contact me kyau har gemun jaririnki yarinka dungurar nonon
- Zaki iya shayar da jaririnki har shekaru biyu, hakan zai baki kariya daga ciwon cancer nono data sassan haihuwa, tare da kiyayeki daga hatsarin kamuwa da ciwon jijiyoyin jinin zuciya [coronary artery dx]
Kai kuma maigida na dawo gareka ka nuna karamci kasamo mata kayan marmari da fruits da nama akai-akai musamman hanta har sati 6 bayan haihuwarta.
- Kuskure ne baiwa mace maganin dakatar da zubar ruwan nono, kusani physiologic process ne don haka akoya ma macen dabaru, in ciwo yake abada maganin ciwo, amma banda basu hormonal drugs don Allah akiyaye akwai illa karkuje ku lalata musu pituitary gland ku kashesu da ransu, domin shikenan kurum hakan na faruwa mace ta daina haila, ta daina ovulation, ta daina jin sha’awa, ta daina komai irin na mutane rayuwarta ta zama maleji, akwai abinda ake kira sheehan syndrome abinda ake gudu kenan, ahir dinku da baiwa mace maganin tsaida ruwan nono saidai in kasan kai gynecologist ko medical doctor ne.
- Mafi akasarin abinda na kance ga masu zubar ruwan nono shine: su rinka ragesa ahankali suna shan maganin rage zugi Irinsu ibuprofen.
Inkuwa yaye zatai koh kuma jaririn ne ya mutu toh ta samo kabeji madaidaici inda hali tasa a cikin freedge yanda zai dau sanyi, koh kuma a cikin roba koh randa sai ta saka ice block in kuma duk ba halin Ä·anqara ko freezer sai ai amfani dashi a yanda ya samu amma dai a wankesa tukunna.
Daga nan inyai sanyi saiki yagi ganyen dai-dai girman wanda zai rufe nononki rijif.
Saiki dau rigar nononki ki mayar wato kitareshi da ita, kidan tsuke numbern bra din ta yanda zai kamesa amma ba tsam-tsam ba, in kuma zai dameki da ciwo toh sai ki barsa kici gaba da harkokinki har zuwa awa 1 koma 2 ya zamto dai sai kinji ya jike da zufa toh sai kicire saiki canza wani a lokacin koh kuma ki bari sai anjima ki kara sa wani, kar kuma ki rinka takure bra din, ki barta saisa-saisa yanda bazata dameki ba.
Ki rinka yin haka sau 3 a rana safe, rana, yammah kiyita yi kullum har zuwa lokacin koh kwanakin da kikaga ya tsaya ya daina zubar.
Da kun Gane bayanan nawa?
Ayi share wa sauran ‘yan uwa suma su amfana.