Yanda Akeyin Hadaddiyar Cup Cake Mai Dadin Gaske Kuma Cikin Sauki:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na Arewamusix.com
Abubuwan Da Zaki Buƙata Sune:
- Flour rabin loka/mudu
- Butter simas guda 2
- Kwai guda 15
- Sugar gwangwani 2
- Baking powder cokali daya na table spoon
- Flavor quater tea spoon.
Yanda Zaki Hada:
Dafarko zaki samu kwano koh roba mai kyau saiki zuba Butter dinnan duka a ciki sannan ki zuba Sugar, ki juya su ki yi ta bugashi domin Sugar din ya narke, toh daga nan sai ki zuba kwai kiyi ta buga shi sosai, idan kina da Mixer ma zai fi haduwa sosai, sai ki zuba flour da baking powder da flavor kiyi
ta bugawa, har sai kin ga ya hade jikinshi, wasu kuma suna zuba flavor da baking powder a flour ne kafin su juye, toh sai ki samu murfi ki rufe, ki je ki kunna oven, idan
gwangwanin cake kike dashi sai ki shafa Butter
koh kuma mai, idan kuma cup cake kike dashi sai ki
zuba kwabin ki sa a Oven ki gasashi.
Note: Amma flavor na gari zaki yi amfani dashi, sannan
idan kika cika domin kiyi gwaninta toh lallai zayyi
caccaki-caccaki a saman cake din, sannan kuma Baking Powder din na gwangwani zaki yi
amfani dashi, bawai na roba ba, domin shine zai sashi ya tashi sosai, wannan shine the most simplest way na yin cake gaskiya.
Ki gwada kiyi dan kadan zaki ga canji, koh baki sa
madara ba zaiyi dadi, idan kuma zaki yi dan kadan ga yawan da zaki
sa abubuwa saboda kada kiyi dayawa yazo
baiyi Miki kyau ba ki yi asaran kayanki.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.