Yanda Zaku Hada Maganin Dandruff, Kaikayin Kai Sannan Kuma Gashinki Yayi Baki Da Tsawo Da Laushi
Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu Mai albarka na arewamusix.com
Ga wanda ke fama da dandruff wanda yake fitar da farin abu a kai, koh kuma gashin kai yake karyewa koh yake saka maka ciwon kai koh kai-kayi koh ciwon idanu toh kusha kuriminku, domin ga magani in shaa Allah.
Idan namiji ne zai rage gashin kansa, mace kuma zata tsefe gashin.
Za’a samu ‘ya’yan hulba babban chokali 1 za’a dafa da ruwa kofi biyu bayan ya wuce kadan, dadan sauran duminsa sai a wanke kai din dashi da safe da dare na tsawon sati daya in shaa Allahu za’a samu abinda akeso.
Sannan a rinka shafe kai da man darbejiya koh kuma a rinka yin kitso dashi shima yana magance wannan matsalar in shaa Allah.
Yanda Zakiyi Hadin Karawa Gashi Tsawo:
Da yawan mata suna da burin mallakar gashi mai tsawo da sheki da kuma laushi irin na matan indiyawa, kasancewar gashi yana daya daga cikin abubuwan dake karawa mata kima, kyau da kuma martaba a wurin jama’a, idan ta wannan ne toh sai muce abu ne mai sauki, abin da ake so kawai shine, yakamata ki rinka kula da gashinki sosai, wannan hadin da zan yi bayaninsa a gaba zai dada sanya gashinki ya kara tsawo da laushi da kuma sheki da yardar Allah, zai kuma hana gashinki karyewa, ina son ki sani cewa wannan hadin akan yi amfani da shine kamar sau 2 a wata, idan kin kasance mai yin amfani da wani hadi na daban ne wanda ba wannan ba, toh bai kamata ki rinka hada wannan salon gyaran gashin da wani na daban ba, inba haka ba kuma sai kiga kwalliyarki ba ta biya kudin sabulu ba.
Abubuwan Da Zaku bukata:
- Man Amla
- Zuma
- Ruwan dumi
Yanda Zaku Hada
Zaki zuba cokalin Amla biyu a roba, sannan ki zuba rabin cokalin zuma a cikin amla din, sai ki sanya cokalin ruwan dumi kamar cokali biyu zuwa uku, toh daga nan saiki rinka juya hadin har sai ya cakudu sosai, saiki taje gashinki kafin ki shafa wannan hadin a fatar kai, toh sannan saiki dan jira na tsawon minti 30, saiki wanke kan da man wanke gashi wato (shampoo).
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.