Yanda Ake Amfani Da Kwai Wajen Gyaran Fuska Fidda Kuraje Da Fitarda Tabbai:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na arewamusix.com
A hakikanin gaskiya kurajen fuska yana daya daga cikin ababen dake bata fuska, da akwai wadansu kuraje masu yawan naci, saboda haka yakamata mu kula da fuskarmu sosai musamman ma a lokacin damina saboda a lokacin ne fuska take fitar da gishiri wato a turance ‘sebum’, kamar yanda muka sani, shi gishirin fuska na toshe ramukan da gumi wato zufa ke fitowa, toh idan hakan ya faru, sai fuska ta fara yin kuraje wannan shine.
Abubuwan Da Ake Buƙata Sune:
- Kwanuka guda biyu
- kwai guda daya
- Takardar ‘tissue’ guda daya
Amfanin Kwai A Fuska:
- Ruwan kwai yana da sinadarin gina jiki da sinadarin vitamin da kuma ‘minerals’
- Sannan kuma yana kare fuska daga kuraje.
- Yana sa kyan Fuska da kuma rage tsufar fuska.
- Har ila yau kuma yana karawa fuska haske.
- Yana rage kumburin ido.
Za’a samu kwano daya sai a zuba ruwan zafi, wanda dashi ne za’a turara fuskar, kwano na 2 kuma sai a zuba ruwan kwai bayan an cire gwaiduwar, sannan a shafa ruwan ‘rose water’ saboda samun biyan bukata.
Ga Hadin:
Dafarko za’a fasa kwai a cire gwaiduwar, sai a kada farin ruwan kwan har sai yayi kumfa, toh daga nan sai a shafa ruwan kwan a fuskar musamman ma a kan kurajen.
A yagi takardar ‘tissue paper’ kadan, sai a manna a fuskar daga kan hanci har izuwa kumatu, a kara daura wata takardar ‘tissue paper’ din a kan wanda aka manna a fuskar tun a farko, wato hawa biyu kenan, sannan kada a yi dariya koh magana bayan an gama manna takardar ‘tissue paper’, din saboda yin hakan zai iya bude fuska, wanda kuma ana sanya takardar tissue paper din ne domin ya matse fuska, toh bayan hadin ya bushe, sai a wanke fuskar, sannan a shafa gwaiduwar kwan a fuska har na tsawon minti Goma sha biyar sai a wanke.
Matsalar kuraje da tabon fuska sunfi shafar matasa, mata da maza, wani lokacin sai an sha wahalar magance kurajen fuska, amma sai tabo ya ki bacewa, rashin bacewar tabon a fuska na bata kwalliya sosai, sau da yawa za’a ga ba’a son shiga taron mutane domin wa’innan tabbon, da yawan mutane sun gwada mayukan kantin, domin rabuwa da tabon fuska, wasu sun yi sa’a wasu kuma ba suyi sa’a ba, toh a yau nazo da bayanin yanda za’a magance tabon fuskar in shaa Allah, ina son a san kusancewa daya za’a zaba daga cikin hanyoyin da zan lissafo, kada a hada su gaba daya ayi domin yin hakan zai kara la’anta muku fuska ne.
- Za’a samu ganyen dogonyaro, a hada shi da kurkum, sannan a shafa a fuska, a jira tsawon harna tsawon minti Goma sha biyar sannan a wanke da ruwan dumi.
- Za Kuma a iya shafa markadadden dankalin Turawa a kan tabon hakan na magance kurajen fuska sosai, sannan ya hana su sake fitowa.
- Za’a daka tafarnuwa sai a shafa a kan tabon, tafarnuwa tana wari, amma tana gyara fuska sosai sannan tana magance tabon fuska fiyeda yanda kuke tsammani.
- Za’a hada karas da tafarnuwa da zuma a shafashi a fuska harna tsawon minti ashirin kafin a wanke.
- A samu hoda ‘baking soda’, sai a hada ta da ruwa, sannan a shafa a fuska na tsayin minti 2 ko 3, daga nan a wanke fuska da ruwan dumi Shima, toh in shaa Allahu idan akayi za’a samu abinda ake BuÆ™ata.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.