Yanda Zakuyi Maganin Ciwon Kai Mai Tsananin Gaske A Cikin Gidajenku:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na arewamusix.com

Shin Menenema Yake Kawo Ciwon Kai? Kuma Taya Za’a Maganceshi Da Maganin Gargajiya?

Shi cwon kai koda yaushe ana rarraba shi azaman na wanda aka saba gani koh kuma wanda ba kasafai yake faruwa ba, amman ciwon kai shine ciwon kai wanda ba wani yanayi koh kuma rashin lafiya daya haifar dashi ba.

Akwai nau’ikan ciwon kai da yawan haske, toh amma akwai nau’ikanshi guda huɗu na Farko shine.

  1. Sinus-
  2. Tension
  3. Migraine
  4. Cluster.

Abubuwan da ake bukata domin a hada wa’innan magungunan da kuma yanda za’a shirya maganin:

  1. Danyan citta cokali daya, idan kuma busasshene toh karamin cokali.
  2. Iklilil jabal, wato Wanda a harshen turance ake Kiranshi da (Rosemary).
  3. Lavender, wanda ake kira da harshen larabci cewa (Kazama).
  4. Yansun

Ga yanda za’a hada, Za’a zuba karamin cokali na sauran maganin amma banda danyar citta, za’a zuba cokali daya ne ita, amma kuma kada amanta, abaya munce idan busasshene karamin cokali, koh kuma rabin cokali ya isa karkizo ku cika.

Za’a tafasa ruwa sai azuba ruwan dumi akai, amma wanda aka dafa sosai, bayan anzuba sai a rufe abarshi yadanyi ‘yan mintuna, toh bayan mintina kadan din sai atace arinka shan kadan lokaci bayan lokaci, in alayi hakan ns shaa Allahu akarshe za’aga sakamako mai kyau da yardar Allah.

Baya wadancan abubuwan dana zayyana a sama, za’a iya samun ingantaccen man tafarnuwa, wanda aka tabbatar da sahihancin shi.

Shi wannan man tafarnuwar za’a rinka shafa shine a goshi idan za’aje barci, wato in za’a kwanta.

Ga Wani Maganin Ciwon Kai Mai Tsananin Gaske Shima Idan Kana Famada irin haka idan har ka jaraba toh in shaa Allahu ciwon kan zai tafi ya barka da izinin Allah.

Shi ciwon kai yana daga cikin chutukan da ake fama dasu na yau da kullum, kuma yana da dalilai koh Musabbabai da yawa, toh amma ga wasu fa’idodi masu albarka a jarraba In shaa Allahu za’a dace

  1. Suratul Fatiha: Malaman Musulunci sun ce lallai fatiha tana maganin kowacce irin cuta ajikin ‘Dan Adam, yanda za’ayi amfani dashi domin magance matsalar ciwon kai kuwa shine, za’ayi bismllah a sanya hannun dama a rike goshin koh kuma wajen da yafi ciwon sai a karanta Fatiha kafa 1 sannan ka saki kan toh in shaa Allahu zaka ji ya daina in shaa Allah.

Amma idan kuma bai daina ba, a sake rikewa sannan a karanta Fatiha din kafa 3 za’aji ya daina, idan kuma bai daina ba, toh a karanta kafa biyar, idan.shima anyi bai dainaba, toh a karanta kafa bakwai. In Allah ya yarda za’aji an warke nan take da ikon Allah.

  1. Man Habbatusswaudah za’a samu Man Habbatusswaudah a zuba acikin Garwashi wato rushi, sannan a rinka shekar hayakin. In shaa Allahu za’aji babu ciwon kan.
  2. Man Tafarnuwa ma gelo: Kowannensu idan aka shafa za’a samu waraka daga ciwon kan in shaa Allahu.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.

Apply Now

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button