Kalaman Soyayya Masu Taushi Da Ratsa Zuciyar Masoya:

Assalamu alaikum warahmatullah jama’a barkanmu da warhaka sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na arewamusix.com

Idan kana tare da masoyiyar ka, toh tabbas ya kasance kanayi mata kalamai masu dadi kuma masu jan hankali, wa inda zasu dinga faranta mata rai a koda yaushe.

Gasu Kamar Haka:

Na dade ina kallon taurarin samaniya a yayinda naga wacce tafi kowacce haske, Dana duba sai naga bakowa bace sai ke masoyiyata, so gamon jinine, hakika sonki ya zamto jinin jikina kinfita daban a cikin dukkan sauran mata Ina son ki Nurul kalbi na.

A duk lokacin da na kallleki, sai inga kamar babu kyakykyawar mace sai ke Ki kwantar da hankalinki masoyiyata babu wata a cikin zuciyata sai ke, ke kadai, hakika yadda da amincewarki a gareni, sune zasu tabbatar da soyayyarki ta gaskiya a gareni ina matukar kaunarki farinciki na.

Hakika farin ciki baya dorewa a rayuwa sai tare da bakin ciki, don haka a kowanni hali nake bazan ta6a mantawa dake ba masoyiyata Nakan raba dare ina mai rokon Allah don neman biyan bukata da rokon Allah ya mallakamin ke gimbiyata.

Kamar yanda kowacce bishiya kanyi rassa a sama, kuma tayi saiwa a kasa, haka nan sonki ya mamaye dukkan ilahirin lungu da Sako na jikina.

Soyayya Akwai Dadi:

Ina ma a ce na kasance dake a duk bugun numfashina, kaunarki ce take kara tasiri a cikin ruhina, babban burina na ga bayyanar fitar murmushinki a kan wannan kyakykyawar fuskar taki Mai haske da annuri, ya kuma kasance ni ne sanadin hakan, bana son Allah ya kawo lokacin da za kiyi fushi dani sosai kaina ba zai dauka ba, hakika Allah ya wadata ki da abin da mata da yawa suke nema wato su duk sun rasa Amma ke kanki kin san a cikin jinsinku na mata irinku kadan ne da a ce na iya rubuta labari da a kan fuskarki zan rubuta littafi mai suna kyauta daga Allah, kuma na san zan samu bayanan rubutu kamar guda 3 da
Sararin samaniya na cike da taurari, teku na cike da ruwa, doran kasa kuma yana cike da ciyayi, toh amma ni zuciyata cike take da soyayyarki ba ta gushewa kamar yanda taurari ba sa gushewa a sararin samaniya, ba ta kafe wa kamar yanda teku ba ta kafe wa, haka zalika ba ta bushe wa kamar yanda ciyayi ba, Ina son ki sani soyayyarki dauwamammiya ce a farfajiyar madinan zuciyata, da ace da akwai wanda zai tsaga jikina da ya ga jininki yana gudana Ako ina, a kan kaunarki na manta kaina nakasa Gane wanene ni, kikan hau ingarman doki domin ki taho mafarkina, wannan sunan da kika boye a tafin hannunki idan dare ya yi, ki duba sararin samaniya zakiga mai wannan sunan yana haska duniya masoyiyata, hakika na kasance mai bayyana a mafarkinki kin kasance a fatar lebena, duk wani taku da nayi a doran duniya sai inji takun na iso ni zuwa gare ki, wato sonki ya zamto marurun zuciya ya yi min saka tun asali so ya shige zuciyata yana min suka, ganinki shine babban burina, idanuwana koh da bacci na farka ki amshi soyayyata abadan kada na koka ba ni barinki cikin kunci yaki zo na yi miki tarba ta musamman daga motsin numfashina kika ziyarci rayuwata a matsayin abokiyar rayuwa, sannan a duk zantukana sai na ambace ki, damuwarki a kullum tana cikin tinanina kece jin dadina sannan kuma kece bacin raina ke kadai ce a cikin zuciyata da kalamaina, zabina da jin dadina hadida bacin raina, saboda da ke kawai nake rayuwa, kaunarki ce ke kula da ni take kuma kau da duk wata damuwa daga raina koda a ce babu ni ka san tuwata zan zamana a tare dake na har abada, kamar yanda baki bai isa ya furta ba toh haka shima jiki bai isa ya nuna ba, sannan zuciyata tayi kadan ta kwatanta ruhinki ne kadai ya san yanda nake jinki a sakamakon ziyartar da yake yi wa ruhina a kowanne dare ina sonki ba zan daina sonki ba har abada har karshen rayuwa ta saboda ban isa na daina sonki bama.

Ina son ki sani soyayyata dake ba ta mutuwa sannan kuma ba ta tsoran mutuwa koda kuwa za’a yi mana kwace, koh da zamu mutu koh kuma zamu lalace toh soyayyar mu za ta kasance a raye, ni na bayar da zuciyata na karbi ta ki na kamu da sonki, ki taimaka ki tallafi rayuwata da ta tsunduma a kan tsananin soyayyarki, ki tausayawa zuciyar da ta shagala a kan tsananin soyayyarki kada rintsi koh zugar mahassada ya saki ki guje ni koh kuma ki rage son da kike min, sonki yana dankare a cikin zuciyata kamar yanda kwakwalwa ke dankare a kan dan adam da a ce zan samu ikon fito miki da shi da na yi domin ki kara gazgata tsananin kaunar da nake yi miki ina son ki masoyayita.

Kalaman Soyayya Masu Sanyi Da Ratsa Jiki:

  • Ina son dukkan taurarin da suke a bisan sama, toh amma ba za’a hada son da nakeyi musu da kuma na wanda take a cikin idanuwan ki ba, ina kaunarki.
  • Hakika lokaci yana nan zuwa da zaki mallakawa wani zuciyar ki, ina mai yin kira a gare ki da ki tabbatar da cewa kin mallakawa wanda ba zai raunata zuciyar ki ta hanyar yaudara koh cin amana ba, saboda ita zuciya dayace babu wanda zaki dauko ki sauya a lokacin da bakin ciki da damuwa suka mamaye zuciyar ta ki.
  • A yanzu haka ina cikin farin ciki, shin kin kuwa san mene ne dalilin yin farincikin nawa? Hmmm toh saboda na kasance mai sa’a, shin kin kuwa san tayaya? A saboda Allah yana sona, kin kuwa san me ya sanya na ce haka? Saboda ya bani wata babbar kyauta, kyautar kuwa ba komai bane ba face ke abin kaunata, ina son ki kuma ina kaunarki.
  • A koda yaushe lokaci tashi yake yi tamkar tsuntsu, amma ita soyayyar mu kullum ginuwa take tare da kara samun wajen zama a cikin zuciyoyin mu kada ki manta da ni ki kasance mai yin tunani na kamar yanda nima na kasance a koh da yaushe tunaninki nakeyi.
  • Abin da nakeji a dangane dake gaskiya ne kema na san kin san da hakan cewa ina son ki, a duk lokacin da kika bar ni ba zan iya motsawa koh da nan da can ba, wannan shi ne abin da zai faru da ni a duk lokacin da na rasa ki, karki gujeni abin kaunata.
  • Shi so tamkar wata sarkar zinarie ce da ta daure zuciyoyin mu a waje daya, a dukkan lokacin da kika tsinka waccan sarkar tofa ki tabbatar da cewa tamkar kin kore farin ciki ne daga cikin zuciya ta gaba daya.
  • Ina son ka, mai ya sanya ka ke yin kokwanto a bisa kalmar so da na furtashi zuwa gare ka? Tabbas kaine mutum na farko da haduwata dashi ya kore min bakin ciki da damuwa, ya wanzar da farin ciki a cikin zuciya ta ya yalwata murmushi a saman fuska fiyeda tunanin Mai tunani, ta hakane dalilin da ya sanya na ke kiran ka da jarumina, hakika kayi nasara kayi nasarar jan ra’ayin soyayya ta a kan ka kaine na mallakawa linzamin Dake cikin zuciyata, kaine mutum na farko da na taba furtawa kalmar so kuma a yanzuma zan kara maimaitawa a gare ka na cewa ina son ka Ina son ka fiyeda yanda kake zato da tsammani.
  • Ka amince min muyi tsaftatacciyar soyayya, ai yanzu na gano cewa a duniya babu abin da ya kai samun masoyi dadi, a duk lokacin da na rasaka ban san halin da zan shigaba, daga karshe ina mai sanar da kai cewa buri na yanzu bai wuce na ganin ranar da zaka zamo ango ni kuma na zamo mata a gare ka ba, ina alfahari da kai a duk inda na kasance, ka huta lafiya daga mai son ganin farin cikin ka mai kishinka sannan kuma mai kaunarka a koh wani lokaci.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button