Wasu Daga Cikin Amfanin Bawon Ayaba Ga Lafiyar Dan Adam:

Assalamu alaikum warahmatullah jama’a barkanmu da warhaka sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na arewamusic.com
Bawon ayaba na kunshe da arziki na sunadaran gina jiki wato (nutrients) da kuma masu sanya karfin jiki irinsu (carbohydrates) da akwai ire-iren sinadaran vitamin B6, vitamin B12, magnesium da kuma Potassium wa inda suke da alfanu iri daban-daban ga lafiyar jikin dan Adam.
Ga jerin hanyoyi tara (9) da bawon ayaba yake inganta lafiyar jikin dan Adam.
- Sa hasken hakora: Goga bawon ayaba a hakora sau 1 a kullum har na tsawon sati daya koh da kuwa na minti daya ne, yana matukar kalkale hakora su fita tar kamar haksen walkiya.
- Fitar da tusar jaki: Mulka bawon ayaba yana taimakawa wajen ficewar tusar jaki da kuma hana bayyanar wata sabuwa a jikin dan Adam
- A matsayin ci ma: Ana amfani da bawon ayaba a matsayin abin ci, domin kuwa mutanen kasar Indiya sun gano cewar sanyawa dahuwar kaza bawon ayaba na kara laushin tsokar ta kaza din.
- Sannan ana saraka ga kurajen fuska: Goga bawon ayaba a kurajen fuska cikin minti biyar har na tsawon sati daya, idan kukayi hakan zakusha mamaki da izinin Allah.
- Yana rage yakunewar fata: Hada bawon ayaba tare da kwaiduwar kwai sai kuma a shafa a fuska sannan a wanke da ruwa, yana matukar warware fata kiga fata tayi luwai-luwai ta dinga sheki.
- Yana saurin saukar da buguwa a jiki: Shafa bawon ayaba a wata buguwa koh wani ciwo na jiki yana taimakawa wajen rage radadin ciwon cikin gaggawa da yake kama mutum.
- Yana warkar da cutar makekkero: Bawon ayaba na taimakawa wajen kawar da cutar makekkero wanda turawa suke kiranta da Psoriasis, yana kuma taimakawa wajen rage radadin kaikayi na makeron din.
- Cizon kwaruka: Shafa bawon ayaba akan cizo kamar na sauro yana dauke kaikayin zafin cizon.
- Kyalkyali: Goga bawon ayaba a fatar takalmi, jakar leda koh azurfa yana sanya su zamto cikin kyalkyali a koda yaushe kaga suna haske da sheki.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.