Shawarwari Guda Ashirin (20) Ga Mata Masu Ciki Wato Juna Biyu:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na arewamusix.com
- Kidaure ki bawa abinda ke cikin ki kulawa matuka, saboda kisami lafiya da kubuta keda abinda ke cikinki ta hanyar daukar cikin da mahimmancin gaske
- Sannan ki rinka cin abinci sosai, irin wanda yake gina jiki wto (proteins irinsu, kifi, kwai, wake, alala, nama dadai sauransu), ta yanda zaki sami lafiya tare da abinda yake cikin cikinki
- Har ila yau ki rinka cin kayan mar-mari, kamar su kwadon rama, cucumber, karas, cabbage, koh kuma latas dadai sauran makamantansu a kowace rana.
- Ki rika shan kaman kofi biyu na madara, koh nono a kowace rana in halin hakan ya samu.
- Kada ki rinka shan Tea mai Nescafe, Bournvita, Milo koh ovaltine, sai dai Tea mai madara kawai koh kuma kisha empty da citta da lipton saboda su bournvita na kumbura yaro aciki zakisha wahala wajen nakuda koma akai ga har sai anyi aiki anciro dan da yake cikinki.
- Kada ki rinka shan magani daka ba tare da shawartan likita ba, saboda yin hakan yakan iya cutar da abinda ke cikinki, domin wani maganin na ratsawa har cikin mahaifa ciki kuwa harda maganin gargajiya shiyasa ake haifo wasu yaran da karamin kai, koh datsattsen lebe da hanci dadai makamancin irin hakan.
- Yana da kyau a rage saduwa da Iyali, lokacin da ciki yake awatanni ukun farko, da kuma watanni biyun karshe na haihuwa, yawan aikata hakan yana tasiri ga lafiyarki dana yaron, sannan a watanni ukun farko hakan na iya haddasa zubewar cikin musamman idan mahaifarki batada kwari, shikuma yayin da watanni biyun karshe hakan na iya jawo nakuda ba shiri ki haifi jariri bakwaini saboda lokacin haihuwarshi beyi ba.
- Ki rinka samun isasshen bacci domin rashin yin bacci da wuri zai sanya miki damuwa da yawan kasala, don haka dole ne ki rinka yin bacci na Awa tara a kowace rana, har na tsawon lokacin goyon cikin.
- Kada ki rinka yin aiki mai wahala da d’aga abubuwa masu nauyi, domin hakan zai Iya samar da matsala ga cikin.
- Ki lazimci natsuwa da rashin fushi, sakamakon wasu matsaloli na gida, koh na ‘yaan uwa, saboda ki samu kwanciyar hankali, ana bukatar hakan dan cikin ya kasance yanda akeso, batare da wata matsala ba.
- Kada ki rinka ziyartan marasa lafiya, masu dauke da ciwon da za’a iya kamuwa dashi, don zai zama hatsari agareki da kuma jaririnki.
- Sannan kada ki rinka sanya tufafi masu matse jiki, koh daure ciki da karfi harna tsawon goyon cikin domin yin hakan zai saki gajiya, da shan wahala wajen yin numfashi tare da hajijiya.
- Kada ki rinka sanya takalma masu tsini koh tudu domin hakan zai sabbaba rashin walawa a ga6obin jikinki, wanda hakan zai samaki ciwon baya.
- Dolene ki rinka yawan ziyartan likita akai-akai, tsawon lokacin goyon ciki, sau daya cikin kowani wata musamman cikin wata na shida, da kuma sau daya cikin kowanne sati biyu a wata na bakwai dana takwas, da kuma sau 1 cikin kowani sati a watana tara har zuwa lokacin haihuwa.
- Ki rinka neman abaki gwajin jini dana fitsari kinayi, lokaci zuwa lokaci saboda ki tabbatar cewa jikinki baya dauke da wani ciwon da yaron zai iya kamuwa dashi, kaman ciwon sugar, ciwon hanta dadai makamantansu.
- Dole ne ki dinga yin wanka a kowacce rana sau 1 zuwa 2 ko 3 a duk lokacin tsawon goyon ciki, da lokacin shayarwa, dan ki kare lafiyarki, da na yaronk.
- Ki rinka kula da nononki tun daga wata na biyar da samun ciki saboda shayar da danki nono na asali wato cholesterol ganganci ne awatannin haihuwa mai gida ya rinka tsotson nonon mace saboda colostrum din da ake so yaron ya samu kan iya tahowa a irin wannan lokacin in tsotso yai yawa gaskiya.
- Ki rinka tafiya da kafa a kowacce rana gwargwadon iyawarki cikin gidanki wato kaiwa da dan komowo kamar taku Dari uku hakan zai kyautata miki jinin jiki lokaci zuwa lokaci yanda zai zama abinci ga danki kuma ya sauwake maki wahala yayin haihuwa.
- Ana son haihuwa a asibiti, saboda samun kulawarki data jaririnki, kuma babu laifi ki haihu a gida idan har kin shawarci likitarki ta tabbatar miki da cewa duk abinda ya shafeki da dan yana tafiya dai-dai, kuma tai alkawarin zuwa ta tsaya kanki yayin da kike nakuda harki haihu.
‘Yar Uwa Ki Guji Wadannan Abubuwan:
- Kusantar sinadarai masu cutarwa irinsu warin fenti, maganin 6era dadai sauransu.
- Daukar lokaci wajen yon aiki.
- Dadewa a tsaye.
- Daga abu mai nauyi.
- Zama a wajen da ake yawaita hayaniya koh kuka surutu mai karfi.
- Zama awurin da akwai karan inji koh kide-kide
- Zama a muhallin dake da sanyi da yawa sosai.
- Ya kamata mai ciki ta guji shan ruwa mai sanyi koh yawaita zama a karkashin na’urar AC na tsawon wani lokaci.
- Ki rinka yin ayyukan gida keda kanki bayan kin haihu da yan kwanaki kadan, domin hakan zaisa mahaifarki ta koma yanda take ada, ya karfafa maki gabobin jiki, kuma ya hanaki ciwon ciki da kirji, sannan kuma ya taimaka wajen samar da nono ga jariri.
Don Allah idan namiji ne kai kuma kaga wannan sakon toh ka ilmantar da matarka kuma ka bata hadin kai domin saida taimakon ka sannan komai zai tafi dai-dai.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.