Abubuwan Kwalliya Guda Shida Da Fata Yake Bukata Da Kuma Hanyoyin Da Zaku Magance Yamushewar Fata Lokacin Sanyin Nan

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku a wannan shafi namu Mai albarka na arewamusix.com

Kasancewar yanzu mun shigo lokacin sanyi a wasu bangarori hakan yana haifarwa Fata yamushewa fata, yana da kyau idan kukayi alwala ku sake shafa mai domin yin hakan na ragewa fata gautsi da yamutsewarta, sakamakon hakan ne yasa na kawo muku hanyoyin dazakubi don magance yamushewar fatan kamar haka:

Zaku Samu:

Man ‘moisturizer: yana da kyau ku samu irin wannan man domin yana taimakawa wajen gyaran fata sosai.

Cleanser: Idan zakiyi amfani da ruwan goge fuska toh ku samu wadanda sinadaransu basuda karfi domin idan sunada karfi suna haifarda yamushewar fuska.

Sannan kuma yana da kyau ku kasance kuna amfani da sabulu wanda sinadaransa basu da karfi, Ina nufin kamar amfani da sabulun jarirai wajen wanke fuska.

A wannan lokacin na sanyi fata na yawan yin duhu yana da kyau ya kasance kuna yin dilka da kurkum domin taimakawa wajen haskaka fatarku a gargajiyance kenan.

Man kade: Za’a iya amfani da man kade a fata, ki hada shi da man zaitun sannan ki rinka shafawa, ko kuma ku narka sai ku zuba a man shafawa yin hakan Yana rage masa wari.

Glycerin: Shi wannan domin kaushin kafa ne, zaku iya gauraya shi da man basilin sannan ku wanke kafa da dutsen goge kafa da ruwan dumi, bayan haka sai ku shafa a tafin kafa sannan ku saka safa , yin hakan za’a rinka yi domin rage kaushin kafa.

Abubuwan Kwalliya Da Fata Yake Bukata:

Ga Kadan daga cikin mayukan da idan ana yawan shafasu suke haifarwa mutum kuraje

Ayau lokacin Nan mun iske kanmu da nau’o’in man shafawa kala-kala da mata da dama basu san da me ake hada mayukan ba, su dai daga ganin yayi kyau sai a ce zai yi wa fata kyau wanda yin hakan babban kuskure ne.

Yawan shafa irin wadannan mayukan da zan kawo suna haifar da kuraje wadanda basu taba barin fuska, in kuma sun bar fuska toh tabonahi baya barin fuskar baya bacewa.

A saboda hakanne yau na kawo muku abubuwan kwalliya guda shida wadanda koh a gida zaku iya hadasu don samun fata mai laushi kuma mara kuraje.

Man zaituun: man zaituun yana dauke da sinadarin rage maiko a fuska, don haka yana da kyau idan za a sake yin kwalliya a samu auduga a tsoma a cikin man zaituun a rinka goge fuskar da ita kafin a sake yin wata kwalliyar, yin hakan yana hana fesowar kuraje a fuska.

Kwakwa: zakiga mace fara kyakkyawa amma da za’a taba hannunta sai aji kamar tana faskare ko surfe saboda tsabagen tauri, kamar wacce takeyin aikin karfi, toh idan kinada irin wannan matsalar zaki samu kwakwa ki kankare bayanta sannan ki markada da ruwa kadan ki tace kisa a firij, idan yayi sanyi sosai sai ki rinka shafawa a tafin hannunki yin hakan nasaka fatar hannu tayi taushi da laushi.

Suga da zuma: Idan mutum na fama da fata mai yawan safa musamman fatar fuska, toh sai ya hada zuma da suga a wuri daya sai ya rinka shafawa a fuska na tsawon minti 30 kafin ya murza a fuskar, yin hakan na cire fatar data mace a fuska don ba sabuwar fata waje, idan kuma an gama sai a wanke da ruwan dumi.

Zaki samu kindirmonki Mai kyau shi kindirmo yana sa fatar fuska laushi da sulbi, sannan ki samu kindirmo ki shafa a fuska na tsawon minti 30 a kullum kafin ki kwanta barci, shi yin hakan na kashe kowace irin kwayar cutar da take fesowa a fuska koh a fata.

Kwai: Ki samu ruwan kwai ki cire kwaiduwar ki rinka bugawa har sai ya yi kumfa, sannan ki shafa a gashin kai na tsawon awa daya ko rabin awa sannan ki wanke da man wanke gashi, yin hakan na cire daudar dake cikin gashi da kuma hana gashi karyewa.

Fiya: Shima yana gyara gashi sosai, idan kika samu fiya kika kwaba shi yayi laushi sannan ki shafa a fatar kai don hana fesowar amosanin kai, ki barshi a fatar kai na tsawon minti 30 kafin ki wanke da ruwan dumi.

Ayi share wa sauran ‘yan uwa suma su amfana.

Apply Now

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button