Yanda Zakuyi Maganin Gishirin Hanci Da Kurajen Dake Fesowa Akan Hanci:
Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu Mai albarka na arewamusix.com
Shi wannan matsalar ba mata kadai ya shafa ba, domin wasu mazajen ma suna fuskantar wadannan matsalolin, bayan mutum yayi gumin fuska idan wannan gumin ya bushe sai kuga wani abu kamar gishiri a kan hanci toh idan baku dauki mataki da wuri ba hakan shike janyo kurajen hanci wadanda idan har sun fito sukan jima kafin su bar fuskarki, akwai wadanda ke daukar shekaru kafin su bace, don haka a yau na kawo muku hanyoyi mafi sauki da zakubi domin magance wadannan abubuwan.
Dafarko dai ga hanyoyin da suka kamata kubi domin magance matsalar:
- Ku rage yawan shiga rana idan rana tayi zafi, saboda idan an shiga rana shine yakan janyo zufa hakan kuma na haifar da wadannan kurajen, don haka ana amfani da man ‘sunscreen’ awa daya kafin a shiga rana.
- Sannan za’a iya tafasa ruwa sannan a rufe fuska da tawul a bokitin ruwan zafin domin turara fuskar a kullum kafin a shiga wanka, yin hakan yana fitar da maikon fuskar dake haifar da gishirin hanci tare dashi kanshi kurajen kan hancin.
- Sai kuma koren ganyen shayi na magance wadannan matsalolin Shima, za’a tafasa ruwa tare da ganyen shayi sannan a turara fuskar dashi koh kuma ana goga ruwan da auduga safe da yamma a kullum kafin a kwanta yin barci.
- Yin amfani da man zaitun da ruwan lemun tsami na warkar da wadannan cutukan, ki matse ruwan lemun tsami a cikin zuma sannan a rinka shafawa a fuskar, sannan a shafa bayan yayi mintuna 15 sannan sai a wanke da ruwan dumi.
- Sannan za’a iya amfani da ruwan kwai da zuma, idan aka hadasu sai a shafa a fuska ya jima kamar na mintuna talatin kafin a wanke da ruwan dumin.
- Sannan kada a manta a duk lokacin da akayi amfani da ruwan dumi, ana son a sake wanke fuskar da ruwan sanyi domin rufe ramukan da gumi da dattin dake shiga ciki.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.