Amfanin Bagaruwa Wajen Gyaran Mace Matsi Da Kuma Tsaftar Farji:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na arewamusix.com
Dafarko dai ana yin amfani da bagaruwa domin maganin kuna sakamakon yanda muke amfani da wuta a yau da kullum, musamman ma mu mata, toh idan har aka samu tsautsayi aka kone, za’a iya amfani da bagaruwa domin samun waraka daga kunan in shaa Allahu.
Yanda mutum zaiyi amfani da bagaruwa domin samun waraka daga konewa kuwa shine, ya samu ‘ya’yan bagaruwa da suka bushe, sai ya daka ‘ya’yan bagaruwar ya rinka zubawa a wajen da ya kone din, Amma idan kuma bai samu busassun ‘ya’yan bagaruwar ba, duk da haka zai iya amfani da danyen ‘ya’yan.
Sai ya samu danyun ‘ya’yan bagaruwar ya rinka matsa ruwansu akan kunan, toh idan yayi hakan zai samu waraka da yardar Allah.
Sannan kuma ana amfani da bagaruwa domin samun fararen hakora, kaga hakora sunyi matukar haske.
Muna kyautata zaton daku masu karatu idan kukaga wannan kanun, hankalinku zai koma kanshi, sakamakon binciken masanan dana kawo muku su a sama a game da yanda bagaruwa ke samar da fararen hakora, domin samun wannan fa’ida ta bagaruwa sai ku samun iccen bagaruwa ku rinka yin asawaki da shi, musamman ace ka daure ka rinka yin aswaki da iccen bagaruwar a kullum, kuma zai fi kyau ka yi hakan sau 2 a kowacce rana, da daddare kafin ka kwanta barci, sannan kuma da safe bayan ka tashi daga barci.
Hanya ta biyu da za’a iya amfani da bagaruwa don samun fararen hakora kuwa itace, ka samu sassaken bagaruwa ka hada shi da jar kanwa ka jika, ka bar su su jika sosai, sai ka dinga kuskure bakinka dashi a kowacce rana, shima wannan ana son kayi hakan yayin da za ka kwanta da kuma bayan ka tashi daga barci.
Haka zalika bagaruwa na samar da matsi ga mata duk matan da su ka amsa sunansu, basa yin sake da gyaran jikinsu domin gamsar da mazajensu yayin ibadar aure, mata za su iya amfani da bagaruwa domin matse kansu, yanda zasuyi kuwa shine, su samu ‘ya’yan bagaruwa da sassakenta sai su hada da Rihatul-hulbi su zuba a cikin tukunya su dora a kan wuta bayan sun zuba ruwa dai-dai misali, idan suka tafasa sai su sauke sannan su tace su zuba shi cikin buta su dinga tsarki akai-akai, toh indai maganar matsi ne, zaki bada labari domin zaki matse gam, domin kuwa wannan hadin bagaruwa na matse mace sosai da sosai.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.