Wasu Hanyoyi Da Zakubi Wajen Rage Kiba Da Tumbi Cikin Sauki:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na arewamusix.com
Wannan hanyoyin da zan fada mukushi in shaa Allahu idan kukayi zakusha mamaki.
Rage Kiba:
Toh dafarko dai zaki zama mai yawan motsa jikinki wajen ( training ).
Na biyu Kuma zaki samu wadannan sirrin kina yin shayi kina sha safe da yamma.
Abubuwan Buƙata Sune:
- Shayi ba madara
- Lipton_
- Lemun tsami
- Na’a-na’a
Da farko zaki tafasa shayi ba madara tare da Lipton da na’a-na’a da kayan kamshi duk a ciki, sai ki matse lemun tsami a ciki ki sa sugar ki rinka sha safe da yamma tare da yawan motsa jinkinki a duk lokacin da kika sha, toh kuwa in shaa Allahu Zaki ga yanda jikinki zai komo bayan wata daya.
Ga Na Rage Tumbi Shima:
Dafarko zaki tanadi ​lemun zaki​ da ​citta​ ki tafasasu minti hudu zuwa biyar kiyi shayi ban da madara ki zuba ma’ul khal cokali daya koh cokali biyu cikin kofin shayin kisha da ganyen shayi kamar ​Lipton​ da zuma ko suga Zakuyi haka sau biyu a kullum Haka kuma za ki iya amfani da ​lemun tsami​ amadadin ​ma’ul khal din sannan bayan haka kuma mutum ya rinka motsa jiki a kai a kai Idan kina ganin cewa ba ki da lokacin motsa jiki toh sai ki rika gudanar da wasu aikace aikacen gida da kan ki.​
Bayan wannan Kuma za ki iya​ ​samun ​kwayar ‘ya’yan Zogalea ki markada​ ​ki hada da ruwan zafi ki rinka sha da safe da dare yana maganin rage kiba koh tumbi sosan Gaske.
Sai Kuma:
- Hulba
- Garin na’a-na’a
- Garin kanun fari
- Zuma
- Lemun tsami
- Farin kwalli
- Manna’a-na’a
Ki hada wadannan ganye guri 1 ki tafasa ki samu farin kwalli wato tozali dunkulen zaki saka a ciki, idan ya kai kamar minti 5 sa ki cire, sannan ki saka zuma a cikin ruwan sha.
ki samu man na’a-na’a ki rinka shafawa, tumbi ki zai ragu insha Allah idan kuma anason rage kiba ne za ‘a rinka zuba lemun tsami a cikinshi
Ganyen na’a na’a kamar guda Goma zuwa goma sha biyu
- Cucumber guda daya dan madaidaci
- Lemun tsami guda daya.
- Danyar cittamar kadadde cikin karamin cokali.
- Ruwa lita 2
Yanda Zaku Hada:
Za’a Jikasu gaba daya kayan hadin a cikin ruwa da daddare ya kwana, idan ya kwana washe gari ayi ta shanshi a matsayin ruwa.
Za’ayi ta maimaita hakan har sai an samu yanda ake so da izinin Allah.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.