Yanda Zaku Kare Kanku Daga Kamuwa Da Ciwon Sanyi Wato (infection):

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi Mai albarka na arewamusix.com

Shi ciwon sanyin mata wata babbar matsala ce da take addabar mata, sannan mafi akasarin mata na fama da wannan cutar, daga kauye zuwa birni, matan aure da ‘yan mata, kafin nayi wannan rubutun sai dana tattauna da mata dayawa akan wace irin cuta ce tafi damun mata a yanzu? Amsar dana samu daga garesu kuwa shine ‘ciwon sanyi’.

Toh Wai Shin Menene Ma Ciwon Sanyi? Sannan Meyake Kawo Shi? Kuma Menene maganinta? Sannan Taya Za’a Kare Kai Daga Kamuwa Da ita?

Domin samun amsoshin wannan tambayoyin ku biyoni muje.

Menene Ciwon Sanyi?

Shi ciwon sanyi, koh ace toilet infection koh kuma vaginal infection duk suna nuni akan abu dayane. Ciwon sanyi wasu kwayoyin cutace datake addabar farjin mata, wannan kwayoyin cutar na hana mace sukuni ta hanyar janyo kaikayin gaba, warin gaba, fesowar kuraje, fitowar ruwa fari koh yellow koh kore, jin zafi yayinda ake jima’i, jin zafi yayin da ake yin fitsari dadai sauransu.

Ire-iren Ciwon Sanyi:

Akwai ciwon sanyin dake damun mata bincike ya nuna kala-kala ne, toh amma zan dan takaita akan guda 3 wanda sune sukafi cutar da mata a zamaninnan.

  1. Wanda bacteriya take janyowa (Bacterial vaginosis): Shi wannan yana daya daga cikin manya-manyan dake janyo wannan cutar, a cikin mata 100 dasukeda ciwon sanyi, kashi 50 suna dauke da bacterial vsginosis, wannan Kuma yana faruwa ne saboda yanayin canji na bacteriya din dake jikin mace, asali akwai bacteriya masu bada kariya a farjin mace wanda ake kira da “normal flora”. Idan wannan bacteriya suka habaka suka yadu sukan zama kwayoyin cuta kaman ‘Gardnerella vaginalis’ sai su haifar da ciwon sanyi.

Toh Taya Ake Kamuwa Dashi Wannan cutar?

Su hanyoyin da ake kamuwa da wannan ciwon sanyi na bacterial vaginosis sune kamar haka,

  • Yanayin yanda mace take tsaftace farjinta
  • Amfani da abubuwan tsarin iyali kaman su implanin, intrauterine device (IUD).
  • Ciki wato mace mai juna biyu.
  • Mu’amala da maza dayawa.

Alamomin Bacterial Vaginosis Sune:

  • Jin zafi lokacin yin fitsari
  • Fitan farin ruwa mai karnin kifi musamman lokacin da ake yin jima’i.
  • Fitan ruwa marar kauri sosai kaman kunu.
  • Kaikayin gaba.

Maganin Bactelrial Vaginosis Kuma Sune:

  • Metronidazole (Flagyl) idan kinada ciki daya haura wata 3 kada kiyi amfani da wannan maganin.
  • Clindamycin (cleacin)
  1. Wanda fungi ke janyowa (Yeast Infection ko Candidiasis)

Wannan kalan ciwon sanyin na faruwa ne sakamakon girman kwayoyin cutar ‘fungus’ wato Candida albicans a cikin farjin mace, shi asali farjin mace yana daukene da wannan kwayoyin halittar amma basa cutarwa har sai sun kara yawa sannan, suna kara yawa ne idan suka samu damshi, koh waje marar iska, wannan kwayoyin cutar ba farji kadai suke tsayawa ba suna iya yaduwa a cikin jikin mutum, sannan mata da yawa suna kamuwa da wannan cutar a wani lokaci a rayuwarsu, domin a cikin kashi 100 kashi 75 sun kamu da shi, cuta ce mai hatsarin gaske idan ba’a maganceta da wuri ba musamman ga masu ciki, ciwon suga koh kuma masu dauke da cuta mai karya garkuwan jiki wato HIV.

Amma ciwon sanyi na Yeast, ba ciwon da namiji sai iya dauka bane bayan jima’i duk da cewa bincike ya nuna a cikin kashi 15 cikin 100 na maza na samun kaikayin gaba koh fesowar kuraje bayan saduwa da macen dake dauke da wannan cutar.

Alamomin Cutar Yeast Infection Kuwa Sune:

  • Kaikayin gaba
  • Radadi a farji
  • Fitan farin ruwa mai kauri, koh mai yanayi kamar awara.
  • Jin zafi yayin jima’i
  • Labben farji suyi jajir koh su kwaile
  • Fesowar kuraje.

Maganin Cutar Yeast Infection Kuwa Sune:

Akwai magungunan da zaki sha domin magance wannan matsalar cutar

  • Fluconazole (Diflucan) koh
  • Itraconazole (Sporanox)
    Likita zai muku bayani akan yanda zaku sha magungunan.

Sannan idan cutar bata fara karfi ba akwai wasu magungunan da zakiyi amfani dasu, wannan sakawa a keyi a cikin farji, akwai vaginal tablets koh kuma creams na kwana 7 zuwa 14 ya dai danganta da yanda likita yace kiyi amfani dashi, kuma koda kin fara amfani dashi sai kikaji sauki bayan kwana 2 ko 3 kada ki daina amfani dashi ki cigaba dasha har sai kin gama dose din sabado idan cutar bata mutu ba zata iya dawo Miki, saboda daga ciki akwai

  • Nustatin (Mycostatin)
  • Miconazole
  • Clotrimazole ( shi wannan yafi karfi a cikinsu).

Yanada kyau idan kina magance ciwon sanyi toh idan da hali ki canza wandunanki (pants) idan babu hali toh ki wanke su duka da ruwan dumi da Dan gishiri saiki shanyasu a rana.

  1. Sai Kuma Wanda Aka Kamuwa Dashi Ta Hanyar Yin Jima’i:

Wannan kalan ciwon sanyin ana kamuwa dashi ne ta hanyar yin jima’i wato mata zata iya shafawa mijinta idan tana mu’amala da wasu mazajen a waje, haka shima mijin zai iya shafawa matar sa idan shima yanada mata sama da daya koh kuma idan yana neman matan banza a waje.

Shi namiji ba kasaifai yake gane yanada wanann cutar ba saboda alamominta basu cika bayanna a jikin namiji ba, yawanci sai idan ciwon ya bayyana ajikin mace, wajen neman maganin sai ya gane cewa shima yana dauke dashi.

Amma idan anyi sa’a ya bayyana a jikin namiji toh akwai alamomin da za’aji kamar haka:

  • Jin zafi wajen yin fitsari
  • Jin zafi bayan fitan maniyyi
  • Fitan farin ruwa kadan-kadan
  • Kaikayin gaba

Alamomin Na Mata Kuma Sune:

  • Kaikayin gaba
  • Jin zafi wajen yin fitsari
  • Warin gaba
  • Fitan ruwa mai launin yellow koh kore koh kuma fari tass.
  • Kwailewar farji

Yanda zaki magance wannan cutar kuwa shine amfani da wannan magani mai suna (Metronidazole) mata da maza duka zasu iya amfani da wannan maganain matukar suna dauke da wannan cutar, kuma zasu kauracewa saduwa har sai sun warke.

Wasu Alamomin Ciwon Sanyi:

  • Ciwon mara: Ciwon sanyi na janyo ciwon mara sosai koda ba lokacin ala’adar bane
  • Wasa da al’ada: Sai kiga ala’adarki na miki wasa, ko yanayin fitar jini ya karu ba yanda kika Saba gani ba.

Dabi’unmu na yau da kullum da zasu iya janyo wannan cutar na ciwon sanyi da rigakafinsu.

  1. Yanayin Yanda Kike Tsaftace Farjinki:

Wasu matan na amfani da abubuwa da dama wajen tsaftace farjinsu, a ganinsu hakan shine dai-dai, misali kamar amfani da ruwan gishiri, ruwan dettol, ruwan lemun tsami, medicated soaps dadai sauransu, toh gaskiya wannan ba tsaftaceki zasuyi ba, hasalima kina kara batawa farjinki halittarshi ne, kamar yanda mukayi bayani a baya game da normal flora, yawan amfani da abubuwannan na kashe wannan hallitun na normal flora a cikin farjinki. Kuma asali shi farjin mace na tsaftace kansa da kansa a yanayin hallitarsa, saboda haka “yar uwa ki dinga amfani da ruwan dumi kawai wajen tsaftace kanki.

  1. Sai yanayin wanke dubura bayan kinyi bayan gida wato kashi:

Asalin yadda ya dace ki wanke bayan gidanki shine ki fara daga gaba zuwa baya, ma’ana daga farji zuwa dubura. Amma mata da yawa akasin haka sukeyi. Wannan dabi’ar sam bata dace ba. Idan kika fara daga baya kina debo kwayoyin cutar dake cikin bayan gidanki kina aikawa cikin farjinki ne, wanda hakan zai janyo miki da matsala babba, shifa farji baya san bakon abu a tattare dashi tamkar ido haka yake ato.

  1. Yin amfani da bandaki mai datti:

Yawancin mata na daukan ciwon sanyi bayan amfani da bandakunan da mutane dayawa suke amfani wato (public toilet). Shiyasa ake cewa ciwon sanyi toilet infection.

Bandakin tsugunno: Idan misali mace mai wannan cutar tayi fitsari a kasa, sai kema kikaje kika tsugunna, fitsarinki ya taba wajen kuma ya dan fallatso a jikinki tuh fah ‘yar uwa zaki kamu da cutar. Saboda haka idan zaki tsugunna ki tsugunna waje mai keu inda ba’ayi fitsari ba, kuma kiyi hankali kada ya fallatsa a jikinki.

Bandakin zama wato (water system):

Shima kafin ki zauna kisaka tissue a jikin toitle sit din saboda farji a bude yake zai iya dauka kwayoyin cuta cikin sauki daga cikin toilet sit din. Kuma kada ki dade kina zaune akai.

  1. Amfani da turare ko sabulu mai kamshi:

Dayawa mata na da wannan dabi’ar fesa abun kamshi koh kuma wanke farji da sabulu mai kamshi, wanda yin hakan babban kusure ne, saboda su wannan kwayoyin cutar suna girma ne a inda yakeda damshi koh kuma kamshi.

  1. Amfani da jikakken wando:

Amfani da jikakken wando na haifar da cutar ciwon sanyi, saboda kaman yanda mukayi bayani a baya, kwayoyin cutar musaman na yeast na son waje mai damshi. Idan kin gama tsarki yanada mahimmanci daki tsantsane jikinki da tawul mai kyau kafin ki maida wandonki, kuma ki kasance kina amfani da wandon da akayi da auduga (pure cotton) saboda sunfi tsotse damshi akasarin wanda akayi na nylon.
Sannan kindinga shanya wandunanki a rana saboda kashe kwayoyin bacteria akan ki shanya su a inuwa cikin bandaki.

  1. Shan magani ba bisa ka’ida ba:

Mutane nada wata dabi’ar sayan magani barkatai ba tareda sanin likita ba. Misali yawan shan antibiotics da kinga kurji a jikinki koh kina ciwon wuya da sauransu, na janyo infection. Bama vaginal infection kawai ba, harda wasu cuttukan ma na daban, a saboda haka a kiyaye yawan shan antibiotics batare da sanin likita ba gaskiya.

  1. Tsarin iyali.

Idan mace tana tsarin iyali domin samun tazarar haihuwa toh akwai tabbas din da zata iya kamuwa da ciwon sanyi saboda yanayin chanji na kwayoyin hallitar ta (hormones) dinta na shafar farjinta koda kina shan pills, koh kinada implant a hannu, koh kuma an daure bakin mahaifarki da dai sauransu.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.

Apply Now

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button