Yanda Akeyin Hadin Sa Kishiya Tagumi:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na arewamusix.com
Toh dafarko dai shi wanna hadin yana sauko wa mace da ni’ima sosai domin maigida zai ji baya gajiya da kawo miki ziyara.
Abubuwan Da Ake Buƙata Sune:
- Kwakwa
- Dabino
- Madara
Yanda Ake Hadawa:
Zaki markada kwakwa da dabino ki tace ruwan sai ki zuba madara peak ki rinka sha zaki ga abin mamaki da yardar Allah.
Gyaran Jiki:
Shi gyaran jikin mace yana da matukar mahimmanci a tare dake ‘yar uwa kada ki bari fatar jikinki ta koma kamar na wata tsohuwa, ana son a koda wane lokaci fatarki ta kasance tana kyau tana sheiki, ta zama tana glowing, hakan zai sanya koh da wani lokaci mijinki yaji yana son kasancewa a tare dake, kuma koh fita yayi waje babu fatar wata diya mace da zai kalla ta daukar masa hankali saboda yasan ta gidansa a gyare take koda wani lokaci.
Abubuwan Da Ake Buƙata Sune:
- Sabulun salo
- Sabulun gana
- Lemun tsami
- Kurkur.
Zaki hada su guri daya ki rinka wanka dashi, shima wannan hadin yana gyaran jiki sosai
Sannan Zaki Samu:
- Garin alkama
- Zuma
- Madara peak.
Zaki hadasu waje daya ki cakuda su sai ki rinka shafawa, kafin ki shiga wanka ki rinka yin hakan kullum, zaki ga abun mamaki in shaa Allah.
Ga Kuma Na Gyaran Fuska:
Hanyoyin gyaran fuska, fuska tayi kyau tayi sumul tayi haske kurajen fuska su fita.
Zaki Samu:
- Tumatir
- Madara peak
Zaki hadasu guri daya ki kwaba dai-dai gwargwadon yanda zai isheki sai ki shafa a fuska ya samu tsayin mintuna talatin akan fuskar taki sai ki wanke, Shima wannan hadin yana gyara fuska sosai.
Zakuma ki iya yin wannan hadin Shima duk na gyaran fuska ne
Abubuwan Buƙata Sune:
- Lemun tsami
- Zuma
Zaki samu zuma ki matsa lemun tsami a cikinta ki shafata ga fuskar ki kibarshi yasamu tsawon minti ashirin sai ki shafa man zaituun akan fuskar, amma sai bayan kin wanke fuskar
Ga Kuma Na Gyaran Gashi.
Abubuwan Da Ake Buƙata Sune:
- Man kade
- Man zaituun
- Man Habbatusswaudah
Zaki hade su guri daya ki rinka kitso dashi yana saka tsayin gashi sosai da bakin gashi hadida saka gashi yayi laushi.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.