Jerin Kalolin Ruwan Dake Fita Daga Farjin Mace

Assalamu alaikum warahmatullah, barkanmu da sake saduwa daku a wani sabon shirin namu dake zuwar muku a wannan shafi namu mai albarka na arewamusix.com
WANI DALILINE YAKESA MATA KE GANIN FARIN RUWA YANA FITOWA MUSU KAFIN KO BAYAN GANIN PERIOD
DINSU?
Shin Hakan Yana Nufin Akwai Matsalane Atare Dasu Koh Babu Wata Matsala?
- Normally mafi yawancin mata suna samun fitowar farin ruwa a gabansu throughout menstrual circle dinsu.
- Akalla mata dayawa suna ganin farin ruwa mai kauri ko salala, mare launi yana fito musu a kowacce rana, adadin daya kai kimanin cikin shokalin shayi, launin ruwan yana iya sauyawa daga farin madara zuwa farin ruwa, koh kuma baki baki wato (brown).
- Banbancin launin ruwan koh kaurin sa yana ta allaka ne da hormonal changes na jikin mace a lokacin da yake fitowa.
- Wannan fitan farin ruwan da mace take gani ta gaban ta kafin period dinta normal ne, babu wata matsala a tattare da hakan. Process ne da ake kira “Leukorrhea” Wani lokacin yana iya kasance wa yellowish.
- Hakan yana faruwa ne saboda yawan hormones “progesterone” dayake taruwa ajikin ta, a wannan gaban ana kiran yanayin da “luteal phase”
- Wa’ennan hormones kamar su”progesterone” “oestrogen” “androgen” etc sauyin yanayin sune ajikin ta shike sawa tayi ta ganin “vaginal discharge” yana fito mata.
- Idan “estrogen” ne sukayi yawa ajikin mace toh a lokacin, se ruwan ya kasance fari-fari mai yauki sannan
- kuma ruwa ruwa.
- Idan kuma “progesterone” ne sukayi yawa ajikin ta, se ruwan ya kasance farin madara kuma mai kauri-kauri.
- Koma ya launin ruwan ya kasance, fari ne, ruwa-ruwa ne, madara-madara ne, yana da kauri ko akasin haka, muddin baya wari ko karni, gaban mace baya zafi, kaikayi ko radadi, toh wannan normal ne.
- Aikin sa (ruwan) shine yayi flushing duk wani dattin vagina, wasu harmful germs, da sauransu, da kuma yasa vagina ta zama moist all the time, hakan yana nuna alamar the vagina and the reproductive system is healthy and functional.
Shin Wasu Lokuta Ne Yakamata Ki Tsammaci Ganin Farin Ruwa A Gabanki, Sannan Idan Kin Gani Akwai Damuwa Koh Babu??
- Normally mata suna iya samun bushewar gaba kamar na kwana 3 zuwa 4 kowanne bayan yankewar period dinsu. bayan wannan kwanakin, farin ruwa mai danko yakan sake bullowa wanda zaiyi kamar kwana 4 zuwa 5 Kafin ovulation, alama ce ta eggs sun fara developing. ana kiran shi da “follicular phase” that means a lokacin ne “eggs” (for ovulation) suke kokarin girma.
- Idan kuma lokacin ovulation yayi, ruwan se ya
- canza kala daga mai danko zuwa fari mai yauki kuma mara kauri (salala) haka. A wannan lokacin yana kara yawa sosai fiye da na kullum, shi kuma ana kiran shi “egg white” aikin sa shine ya taimaka wajen santsin sperm a vagina da cervix domin ya samu damar isowa wajen kwai da yake jiransa for ovulation.
- Sannan Mata dayawa suna amfani da ganin wannan ruwan a matsayin alama ta ovulation dinsu, hakan yana taimaka musu wajen samun ciki da wuri ko kuma kaura cewa yin cikin. Wannan process din shi ake kira da “natural family planning” ko “fertility awareness method”.
- Idan ruwa-ruwan ya kasance mara kauri (salala) to ana kyautata zaton shine “fertile” (i.e ciki zai iya shiga kenan in kuma kwan ya samu sperm), saboda a lokacin kwan zai sauka zaman jira.
- Idan kuma ruwa-ruwan ya kasance fari mai kauri toh shi kuma shine “infertile” (wanda ko an sadu ciki bazai shiga ba) saboda kwan har ya rika, karfin sa ya kare, yanzu saidai ya harzika yayi facewarsa.
- Toh irin wannan ruwa-ruwan mai kauri zaki cigaba da gani daga bayan ovulation har zuwa wani period din.
- Daga bayan ovulation din zuwa wani period din, yawan fitowar ruwan zai rinka raguwa a hankali, yana zamowa mai kauri kuma mai danqo again, wani lokaci har zaki iya jinsa kamar wata gum ko glue.
- On average dai, yana kaiwa irin kwana 11 zuwa 14. That is tsakanin ovulation dinki zuwa wani period dinki kenan.
- Wasu lokuta kina iya ganinsa yellowish haka kafin period dinkin.
- Idan mace taga wani irin brown discharge a bayan period dinta kuma, bayan jinin ya dauke, se ta sake ganin wani baki-baki haka brown ya zo mata, to shi din yana kasance wa tsohuwar jini ne daya daskare bai samu daman fitowa ba last time. Shine yanzu yake kamo hanya.
- Idan kuma brown discharge din kafin period ne fa? Ko kuma taga jinin Dan digo-digo haka a lokacin da take tsammanin period dinta, to shi
- kuma yana iya kasance wa sign ne na “implantation” daga farko farkon pregnancy. Maza se kiyi kokari kije pregnancy test domin a tabbatar da hakan ko akasin hakan. (In kin samu congratulations )
Meke Jawo Koh Sanadin Fitowar Farin Ruwan A Gaban Mace?
Akwai kamar category guda biyu:
- Akwai wanda yake normal: saboda hormonal
changes. - Akwai kuma wanda yake abnormal: saboda infection.
- NORMAL
- Yana iya kasance wa alama ce ta reproductive system na mace yana functioning properly, saboda kasancewar discharge din mara kauri ne, mai yauki ne kuma mai santsi, sannan baya wari ko karni, wasu suna kiran shi da “egg white mucus”
- Normal side effects na family planning; sakamon sauyin yanayin levels na hormones da yake jawowa, hakan yana sawa normal vaginal discharge ya karu shima.
- Pregnancy: wani lokaci yawan vaginal discharge kafin lokacin normal period dinki yazo yana iya zama sign ne na daukan ciki, musamman ma idan mucus din ya kasance mai kauri kuma ruwan madara madara.
- ABNORMAL:
- STIs(Sexually Transmitted Infections): kamar su Gonorhea, chylamydia, Trichomonas duk suna jawo mace tayi ta ganin fitan ruwa ta gaban ta. Gonorhea da chylamydia su yawanci basa ma nuna symptoms, sannan discharge dinsu yana nan ne yellowish haka kamar diwa-diwa.
- Shi kuma Trichomonas; discharge din da yake jawowa yana yellow ko Kore ne haka, sannan yana nuna symptoms dinsa kamar karnin kifi-kifi kuma ga kaikayin tsiya.
- Candidiasis (yeast infection): shi kuma discharge dinsa fari ne mai kauri, kamar farin madara, yawanci yafi faruwa a lokaci kafin mace taga period dinta. Yana da symptoms kamar kaikayi da jin zafi-zafi a gaban mace (ta ciki da ta wajen).
- Bacterial Vaginosis: shima wata infection dinne da yake jawo discharge mai Kama da toka-toka (gray-white) sannan yana sa warin gaba kamar karnin kifi-kifi haka.
Kamar yadda kuka gani a sama tin farko, ainihin ababen dakesa fitowar farin ruwa kenan da kuma yawancin lokutan da ruwan yake fito ma mata.
SHAWARATA ANAN ITACE:
Duk sanda kika ga ruwa yana fitowa ta gaban ki, inma fari ne, milk-milk ne, mai kauri ne ko salala ne, mai yauki ne ko mai santsi ne, muddin baya wari kuma baya sa kaikayi ko radadi ko jin zafin gaba ko kuma yayin fitsari ko saduwa da miji, kawai ahlun salun yake fitowa abinsa, to karki tada hankali wannan normal ne. Alamace ta jikinki a matsayin kina mace, yana aiki yadda yakamata kuma cikin kocin lafiya
Idan kuma kinga ruwa yana fito maki koma ya launin sa yake, kuma tare da hakan akwai zafin gaba, kaikayin gaba, ko warin gaba, kumburin gaba, kurajen gaba ko dadewar fatar shi, ta ciki ko ta wajensa, ko kuma duka biyun, to maza maza kiyi saurin zuwa asibiti domin abaki magani, wannan shine.
Allah yaba marasu lafiya lafiya, mu da muke da ita Allah yakara mana lafiyar, aamin.