Amfanin Man Kadanya Da Mahimmancinshi Ga Lafiyar Fatar Yara Da Manya Musamman A Lokacin Sanyinnan:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu Mai albarka na arewamusix.com

Man kade yanada matukar amfani a fata domin yana dauke da sinadarai masu yawa har da sinadarin vitamin A da vitamin E

Wannan mai na magance kurajen fuska da gautsin fata kai harma da kyasfi.

Amfani da wannan man kaden yana sanya Fata tayi sulbi.

Kadan Daga Cikin Amfanin Man Kade:

Wannan Hadin Na Magance kyasbi:

Za’a samu man sandal da Kuma man labender a zuba a cikin man kaden sannan a kwaba su sosai sai a samu kwalba mai kyau a zuba hadin a ciki, sai a mayar da wannan mai din man shafawar mutum kullum, za ayi amfani da shi har na tsawon wata shida in shaa Allahu za’a ga chanji.

Yanda Za’a Magance Fata Mai Gautsi:

Dafarko za’a samu man kwakwa da man zaitun da kuma man almond sannan a zuba a kwalba a kuma zuba man kade a ciki, sai a kwaba da cokali ya kwabu sosai sannan a rinka shafawa a jiki, sai amayar da man, man shafawa bayan an yi wanka.

Domin Magance Bushewar lebe Kuma:

Za’a samu zuma da man zaitun sai a zuba a kan man kade a kwaba su sosai, sai asashi a wuri mai sanyi, sannan a rinka shafawa a baki a kullum za’a samu sauki in shaa Allah.

Ga Mazan Da Kuraje Ke Fito Musu Idan Sunyi Aski Suma Ga Yanda Zasu Maganceshi:

Za’a samu man rosemary da man kwakwa sannan a zuba a kan man kade a kwabasu, sai a rinka shafawa a kulum bayan an aske gemun, yana warkar da kurajen da suke fesowa a gemun bayan an yi aski in shaa Allah.

Yanda Ake Amfani Da Man Kade awajen Magance Makekkero:

Za’a samu man kade a hada shi da man zaituun sannan a rinka shafawa a inda makekkeron yake a kullum domin samun biyan bukata.

Yin Kitso Da Man Kade:

Yin kitso da man kade na magance fatar kai daga fitowar makekkero sannan yana sanya gashi laushi da tsayi da kuma sulbi.

Sulbin fata:
Yawaita shafa man kadanya a jiki bayan an yi wanka na sanya sulbin fata sannan yana hana fesowar wadansu cuttukan fata.

Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.

Apply Now

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button