Yanda Zaki Amfani Da Man Kwakwa Domin Rage Tumbi Da Kuma Magance (stretch marks) Wato Nan karwa

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a Wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku a wannan shafi namu Mai albarka na arewamusix.com
Yau iason zanyi mana bayanin yanda ake amfani da man Kwakwa wajen warkar da wasu matsalolin dake damunmu mata, wadanda suka hada da rage tumbi da warkar da nankarwa, wato ‘Stretch mark’ a Turance.
A kan samar da danyen man kwakwa ba tare da kona wani abu daga amfaninshi ba. Bashi da wani wahalar hadawa, ba’a bukatar yin amfani da wuta, kamar yadda na fada muku a baya.
To dafarko dai, uwargida zaki samu kwakwa dai-dai bukata, saiki cire bawonsa, ki yayyanka su kanana, sannan ki markade sosai. Bayan kin markade, sai ki tace ruwan, ki durashi a roba, sannan ki ajiye shi a wuri mai iska, kibar shi ya kwana.
Da safe za ki ga mai ya taso sama, ki sa cokali, ki yade man, ruwan ne kadai zai rage a kasa. Za ki ganshi kamar man shanu, in kuma kina bukata, kafin ki yade man, sai ki saka shi cikin firji don ya yi kankara. Hakan ya fi dadin yadewa, za ki gan shi kamar man kade. Masana sun tabbatar cewa ya fi dafaffen man kwakwan tasiri.
An nuna cewa za a iya shan shi haka nan domin rage tumbi. Baya ga wannan, za a iya amfani da shi wajen magance Amosanin kai, wato ‘Dandruff,’ don haka za a iya amfani da shi a matsayin sinadarin wanke kai (Shampoo). Ko kuma a hada shi da man kitso da man shafawa domin gyaran jiki matukata
Sannan kuma ta bangaren warkar da nankarwa kuwa, babu kamar man kwawa. Da zaran kika fara amfani da shi wajen shafawa a jikinki, tabbas zakiga nankarwa ta fara bacewa daga jikinki.
Don haka a takaice kwakwa da manta suna da matukar amfani ga mace, baicin wadannan da muka lissafa. Ruwan na magance wasu cututtukan jiki, musamman masu cututtuka a mafitsara, wanda ake kira a Turance ;Urinary infections.’
Allah ya ba mu sa’a, Allah ya taimake mu, da fatan za a wuni lafiya.
Man kwakwa ya na da amfani wajen inganta lafiyar fata, gashi, rage nauyin jiki, taimakawa wajen tace abincin jikin mutum da bayar da kariya ga wasu cututtuka da mutum ka iya kamuwa da su. Kiwon lafiya:
Ga wasu kadan daga cikin Amfanin man kwakwa guda 8
1. Gyara fatar jiki Ana amfani da man kwakwan wajen man shafawa a jiki wanda yana da matukar fa’ida ga ma su busashshiyar fatan.
2. Man kwakwa yana kara laushin fata da yadda yake warware tamushewa irin ta tsufa a jikin fata kuma yana fa’idantuwa ga ma su ciwon kyasbi.
3. Man kwakwa yana bunkasa yalwatar gashi kuma ya kawatar da shi wajen kyalli.Yana kuma bayar da kariya ta amosani da rashin karyewar gashi.
4. Yana maganin ciwon zuciya: akwai sindarin lauric acid a cikin man kwakwa wanda ya ke taimakawa wajen rage tasirin hauhawar jini da da rage daskararren maiko wadanda daman su ne ma su assasa ciwon zuciya. Yana kuma fa’idantuwa wajen al’adar mata Wato (period) a turance.
5. Yana rage nauyin jiki Da yawan mutane su na kukan jikin su yana musu nauyi saboda maiko da yawan teba a jikin su, man kwakwa wanda shima maiko ne amma ya na inganta narkewar duk wani daskararren maiko da yake cikin jikin mutum wajen assasa lafiyar kayan cikin mutum.
6. Yana Bada kariya ga cututtuka Man kwakwa yana bayar da garkuwa ga lafiyar jikin mutum sanadiyar sinadarai na lauric acid, capric acid da caprylic acid. Wadannan simadai suna inganta kariya na kananan kwayoyin cututtuka irin su kuraje, cutar sanyi da cutar HIV mai karya garkuwar jikin dan Adam.
7. Yana tace amfanin abinci Akwai ma su fama da ciwon ciki wanda rashin saure tace abinci dasu ka ci ke janyo musu, binciken masana kiwon lafiya ya bayyana ingancin man kwakwa wajen inganta wannan matsala ta rashin tace amfani abinci da wuri a cikin mutum.
8. Domin samun lafiyar Hakori Akwai sinadarin calcium a cikin man kwakwa wanda yake inganta karfin hakori kuma yake bayar da kariya wajen cututtuka na hakori da kara mu su haske su zama farare tar
.