Yanda Zaki Hadin Gyaran Nono Yakoma Tamkar na Budurwa Su Tsaya A Tsaye Kuma Mai Saukin Hadawa:
Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na arewamusix.com
A wannan lokaci zanyi bayani dalla-dalla a kan yanda mace zata gyara nononta yadawo tamkar na budurwa in shaa Allah, wannan ba wani abu ne mai wahala ba, da zarar kin yi amfani da wannan hadin, nononki zai koma ya tsaya cak kamar na budurwa in shaa Allahu.
Ba tare da bata lokaci ba, zan kawo muku yanda zakuyi wadannan hade-haden cikin sauki.
- Gyaran Nono Na Farko
Shi wannan wani hadi ne da masana kiwon lafiya suka samar dashi bayan gudanar da zuzzurfan bincike, kuma babban abin farin cikin game da wanan hadi, bayaga saukin hadawarda yake dashi, shine, an jarraba anga fa’idarsa, sannan bashida wata illah ga lafiyarmu, saboda dukkan kayan hadin dangogin abincin da mu ke ci yau da kullum ne.
Abubuwan Da Za’a Nema:
- Hulba.
- Gyada.
- Alkama
- Ridi.
- Shinkafa.
- Karas.
Duka wadannan kayan abincin ake bukata mace ta tanada, abin da zatayi kuwa shine, ta samu garinsu, kamar shinkafa, sai ta gyara ta sosai ta daka koh takai a nika yanda zata samu garinta, toh haka zatayi wa gyada, ridi, da alkama. Ita kuwa hulba sai ta sayo garinta, shi kuma karas sai ta shanya shi ya bushe sannan ta samu tayi garinsa.
Bayan ta sami garin wadannan kayayyakin dana ambata a sama, sai ta hada su waje daya ta gauraye, daga nan ta adana su a mazubi mai tsafta, kuma mai murfi yanda zatayi amfani da wannan hadin gyaran nono kuwa shine, zata sami madara ‘Peak’ idan son samu ne, ta rinka zuba wa ta sha a kullum, zata sha mamaki matukar ta juri amfani da wannan hadin gyaran nonon, domin kuwa nononta zai dawo tamkar na budurwa, da yardar Allah.
- Yanda Zakiyi Karin Ni’ima:
Toh kamar dai yanda na fada a sama ana samun mata da kan yi kukan rashin ni’ima, wanda hakan kan hana jin dadin jima’i tsakanin ma’aurata, sannan ya haifar da rashin gamsuwa tsakaninsu, toh dan har kina fama da wannan matsala koh matar ka na fama da matsalar rashin ni’ima, sai ka karanta ka fada ma ta don ta hada, saboda a wannan harka ba kunya gaskiya.
Kayan Hadin Da Ake Bukata Sune:
- Ruwan Kankana Kofi 1
- Garin Dabino babban cokali 3
- Zuma babban cokali 3
- Madarar “Peak” rabin gwangwani.
Idan amaryane koh uwargida ta tanadi wadannan abubuwan dana ambato a sama, abin da zatayi kuwa shine, zata cakuda garin dabinonta da ruwan kankana da zuma, ta tabbatar sun gaurayu sosai, sai ta zuba cikin madararta, ta rinka sha, da iznin Allah matsalarta zata kau, shi wannan hadin namiji ma zai iya amfani dashi ba dole sai macene kadai zatayi amfani dashi ba.
Shi kuma wannan hadin, baya ga karin ni’ima da mace zata samu, kuma zai kara mata dadi yamda zata iya gamsar da mijinta.
Kayan Hadin Da AKe Nema:
- Aya babban cokali 5
- Ridi babban cokali 5
- Cikwi babban cokali 3
Yanda zatayi wannan hadin kuwa shine, tun da farko zata gyara ayarta, sannan ta soya ta, bayan haka sai ta daka ayar don ta samu garinta. Shi kuma ridi bayan ta gyara shi ta cire duk wani dattin dake cikinsa, sai ta nika shi don samun garinsa, shi ma cikwi za ta daka shine don samu garinsa.
Bayan ta samu garin wadannan abubuwan 3 dana lissafosu a sama, sai ta hada su waje daya ta gauraya su, ta tabbatar sun gaurayu sosai, sannan ta adana a mazubinta mai kyau.
Abu na gaba kuwa shine, ta samu madara koh nonon shanu mai kyau, sai ta rinka zuba karamin cokali 2 cikin nonon ko madarar, ta rinka sha safe da yamma a kowanne yini, samun ni’ima da gamsuwa yayin jima’i ba sai an fada Miki ba ‘yar uwa.
- Na Karin Sha’awa.
Wasu matan kan yi kukan rashin sha’awar jima’i, akan samu matan dake fama da wannan matsalar da har ta kai ta kawo, a dole take saduwa da mijinta, amma ba wai don ta na da sha’awar jima’in ba. Da iznin Alla idan ta yi wannan hadin tayi amfani da shi za ta kasance mai sha’awar jima’i sosai da sosai.
Kayan Hadin Da Ake Bukata Sune:
- Sassaken Baure babban cokali 5
- Kanimfari babban cokali 3
- Zuma babban cokali 2
- Lipton
Yanda zata hada, zata daka sassaken bauren bayan ta barshi ya bushe don ta samu garinsa. Sai ta daka kanimfari, shi ma don ta samu garinsa, saita gauraya garin kanimfarinta babban cokali 3 da garin bauren babban cokali 5, bayan ta tabbatar sun gaurayu sai ta zuba zuma babban cokali 2 ta cakuda su, su cakudu sosai, sai ta debi karamin cokali daya na wannan hadi ta zuba cikin ruwan lipton ta sha sau biyu a rana.
- Hadin Gamsar Da Maigida.
Kayan Hadin Da AKe Bukata Sune:
- Garin gero (Amma kar a surfa)
- Garin furen(huda) tumfafiya babban cokali 3
- Garin ‘ya’yan zogale babban cokali 3.
Bayan an samu garin wadannan abubuwan sai a gauraya su, mace ta rinka shan karamin cokali sau biyu a rana in shaa Allahu za’a ga chanji.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.