Matasa Dama Ta Samu: An Sake Bude Shirin Bayar Da Horo Akan Technology
Assalamu alaikum barkanmu da wannan lokaci fatan kowa yana lafiya.
Shirin 3 Million Technical Talent (3MTT) na Ma’aikatar Sadarwa, Kirkire-kirkire da Tattalin Arzikin Dijital na Najeriya ya kuduri aniyar habaka kwarewar fasaha a kasa tare da tallafawa hangen nesa na Shugaba Tinubu na samar da ayyukan dijital miliyan 2 zuwa 2025. Shirin zai taimaka wajen tabbatar da Najeriya ta zama jagora a fitar da kwararru a duniya.
- Mataki na farko ya fara a Disamba 2023 tare da hadin gwiwar NITDA, inda aka horar da mutane 30,000 a dukkan jihohi da Abuja. An hada karatun kan layi mai zaman kansa da darussa na fasaha ta zahiri tare da tallafın kungiyoyi fiye da 120.
- Mataki na biyu zai horar da kwararru 270,000 a rukuni uku na 60,000, 90,000, da 120,000.
Wannan matakin zai hada kai da gwamnatocin jihohi, kungiyoyin ci gaba, da cibiyoyin koyo don cimma nasara mai ma’ana.
Aiyukan da za’a koyar
- Cybersecurity
- Game Development
- Software Development
- Al / Machine Learning
- Animation
- Data Analysis & Visualization
- Cloud Computing
- UI/UX Design
- Product Management
- Quality Assurance
- Data Science
- DevOps
Yadda zaku cike
Domin cikewa ku danna Apply dake kasa
APPLY NOW
Domin shiga: https://app.3mtt.training/login
Domin karin bayani: https://3mtt.nitda.gov.ng/