Gwamnatin Tarayya da ITF Sun Kaddamar da Shirin Horas da Matasan Najeria Sanaoin Hannu Skill-Up Artisans

Assalamu alaikum barkanmu da wannan lokaci da fatan Anyi karamar sallah lafiya Allah ya maimaita mana ameen.
Gwamnatin Tarayya, tare da hadin gwiwar Hukumar Industrial Training Fund (|TF), ta kaddamar da shirin horar da matasan Najeriya a fannoni daban-daban na sana’Æ¡’in hannu domin karfafa dogaro da kai. Shirin ya kasu gida uku:
- Masu Sha’awar Koyo (Intending Artisan) Wadanda ke son koyon sabuwar sana’a.
- Kwararrun Masana (Skilled Artisan) Wadanda ke da kwarewa a wata sana’a kuma suke son shiga shirin.
- Cibiyoyin Horaswa (Training Center) Masu bada horo a fannin sana’o’in hannu.
Bayan kammala shirin, mahalarta za su sami takardar shaidar kammalawa tare da tallafin fara kasuwanci domin su ci gaba da aikin da suka koya.
Sana’o’in da za a koyar sune kamar haka:
- Gina da Gine-gine (Building and Construction)
- Gudanar da Masauki da Otal (Hospitality Management) Harkar Wutar Lantarki (Power)
- Fata da Kayan Fata (Leather Works)
- Noma da Harkokin Noma (Agric/Agro Alied)
- Zanen Kaya da Dinki (Fashion Design)
- Fannin Kwamfuta da Sadarwa (ICT)
- Sanao’in Hannu da Fasaha (Arts and Crafts)
- Gyaran Kayan Amfani (Appliance Service Technician) Kawata Ciki da Tsara Gida (lnterior Design)
- Gyaran Motoci (Vehicle Auto Services)
- Kula da Fata da Kyau (Cosmetology)
- Gudanar da Muhalli da Tsare-tsare (Facility Management and Planning)
Yadda Zaka Cike
Domin cikawa danna Link dinnan https://supa.itf.gov.ng/register