Sabbin Bayanai Kan Shirin Tallafin Manoma Na NIYEEDEEP/YEIDEEP Wanda Ya Kamata Kusani

Game da NIYEEDEEP ko YEIDEEP, da fatan za a cike a karkashin daya daga cikin sunayen.
Bayani akan shirin NIYEEDEEP / YEIDEEP
NIYEEDEEP da YEIDEEP abu daya ne. Sai dai sunan NIYEEDEEP ne aka fara amfani da shi, kafin daga baya a maida shi zuwa YEIDEEP. Tun da farko, wadanda suka cike a karkashin sunan NIYEEDEEP, bayan sun kammala cike-cike, an ba su lambar code kuma ana sa ran za su bude asusu a daya daga cikin wadannan bankuna masu zuwa:
- FEDILITY
- LOTUS
- KEYSTONE
Bayan an sauya suna zuwa YEIDEEP, an bude karin bankuna daga guda 3 zuwa 12, domin tabbatar da cewa kowa ya samu saukin shiga wannan shiri mai albarka. Wasu daga cikinku kun riga kun bude asusu ta intanet, amma baku ga asusun nan take ba-kada ku damu, wannan lamari na faruwa ne saboda cunkoson aiki, amma asusunku zai bayyana ba da dadewa ba, in sha Allah. Wasu ma daga cikinku sun riga sun gani tuni, kuma suna ci gaba da amfana. Har yanzu dai akwai kimanin mutane 900,000 da suka saura-wato dama tana nan a bude gare ku. Kada ku bari ta wuce ku! Wannan dama ce ta sauya rayuwa, kuma za ta rufe nan ba da dadewa ba. Ku hanzarta ku shiga kafin lokaci ya kure!
Duk wanda ya cike yanzu, ko aka cike masa a baya, ya tsaya lafiya-In sha Allahu, za a bude masa asusu, kuma za a tura duk abin da ya shafa zuwa gareshi. Abu mafi muhimmanci a nan shi ne lambar wayar da ka yi rajista da ita. Ita ce hanyar da za a iya tuntubar ka da ita, don haka ka tabbata tana kunne kuma ba ta canzawa. Ka kula da asusunka sosai. Ana iya tuntubar ka a kowane lokaci domin karin bayani ko wasu matakai na gaba. Kada ka yi sakaci da wannan dama-ka kasance a shirye!
Jimillar mutane miliyan shida ne za su amfana daga wannan shiri mai albarka-mazaje da mata da suka nuna sha’awar cikawa. Ana sa ran, nan ba da jimawa ba, In sha Allahu, za su fara cin moriyar abin da suka nema. Yanzu haka, sama da miliyan biyar da dubu dari (5.1 million) sun riga sun samu damar cikawa-kuma hakan ya kasance tun daga yau da dare. Har yanzu ana ci gaba da karbar takardun neman cikawa, amma cikawa yanzu ba ta tafiya yadda ake bukata sai da sa’a, musamman a cikin lokutan dare.
Wanda bai cike ba, ya garzaya ya cike yanzu-kar ka bari lokaci ya kure! Kuma ga wanda ya riga ya cike, ya dage da addu’a, Allah Ya sa ya dace da samun wannan dama mai girma.