Tallafin Gwamnati Ga Kananan ‘Yan Kasuwa: Sama da 60,000 A Kyautar MSME Na 2025

Gwamnatin Tarayya ta sanar da bude tashar karɓar aikace-aikace don gasar kyautar MSME ta kasa na shekarar 2025, wadda za ta kasance a bude har zuwa ranar 7 ga Afrilu, 2025. Wannan sanarwa ta zo ne bayan wani taron manema labarai da Kwamitin Shirya Kyautar ya gudanar a ranar Juma’a, 7 ga Maris, 2025.

A cikin makonni uku da suka gabata, sama da aikace-aikace 60,000 daga ‘yan kasuwa masu kananan sana’o’i a fadin kasar nan aka riga aka karɓa. Masana’antu da suka fi shahara a cikin wadanda suka nema sun haɗa da na harkar noma, fasahar bayanai da dijital, da kuma masana’antar kirkira.

A bana, an ƙara wani sabon rukuni a gasar – wanda ya shafi mutanen da ke da nakasa, domin basu dama da tallafi. Sauran rukunin sun hada da:

  • Aikin fata da kayan fata
  • Kayan daki da aikin katako
  • Masana’antu da dinki
  • Kyau da kayan kwalliya

Kyaututtuka Masu Dimbin Amfani

Masu nasara a gasar za su samu kyaututtuka masu tarin yawa da darajarsu ta kai kimanin naira miliyan 700, ciki har da motoci, shaguna da gidaje. Wannan ya nuna himmar Gwamnatin Tarayya da hadin gwiwar masu zaman kansu wajen bunkasa fannin MSME a Najeriya, la’akari da irin rawar da fannin ke takawa wajen ci gaban tattalin arziki da samar da ayyukan yi.

An bukaci kananan ‘yan kasuwa da su ci gaba da tura aikace-aikacensu domin cin moriyar wannan dama mai muhimmanci. Tashar na ci gaba da kasancewa a bude har zuwa ranar Lahadi, 7 ga Afrilu, 2025.

Domin cikewa Danna Link dake kasa

Latsa nan don cikewa: https://msmeclinics.gov.ng/award-apply/

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button