Ga Wasu Tallafi Guda (6) Da Ake Cikewa Daga Gomnatin Tarayya

Assalamu alaikum warahamatullah barkanmu da wannan lokaci da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.
Har yanzu ana cigaba da amfana daga wasu tsare-tsare da gwamnatin tarayya ta samar a karkashin ajandar sabunta fata (Renewed Hope) don saukakawa ‘yan Najeriya a bangarori daban-daban. Kada mu shagala ba tare da mun amfana ba domin gwamnati ta samar da su ne domin mu ‘yan Najeriya. Mu kuma yada wannan sakon don al’ummar mu su amfana.
Shirin Consumer Credit:
Wanda aka samar don don habaka damar samun lamuni ga yan Najeriya masu aiki nan da 2030. Tsarin zai inganta kasuwa tare da samar da jari dan habbaka kasuwanci da tattalin arziki. Masu bukatar kasancewa cikin shirin zasu iya bin wannan adreshin yanar- gizo dake kasa:
Shirin Renewed Hope Cities:
Wannan shiri zai samar da gidaje 100,000 ga yan Najeriya masu matsakaicin karfi. A halin yanzu an soma gudanar da wannan shiri, masu bukata zasu iya bin adreshin yanar-gizo dake kasa:
https://renewedhopehomes.fmhud.gov.ng
Shirin 3 Million Technical Talent (3MTT):
Shima wani muhimmin bangare na ajandar Renewed Hope na shugaba Bola Tinubu da zai samar da kwararrun a bangaren fasahar zamani a Najeriya don karfafa tattalin arzikin mu da kuma sanya Najeriya a matsayin kasa mai wadatar ilimin kimiyyar zamani. Akwai darussa da kuma damammaki da yawa tattare da wannan shirin, matasan da ke sha’awar wannan dama zasu iya cikewa a adreshin yanar-gizo dake kasa:
National Youth Investment Fund – NYIF
Wanda aka tsara don samar da damar samun tallafı, lamuni, da kuma saka hannun jari ga matasan Najeriya. An ware wa wannan asusun jimillar kudi har Naira biliyan 110 da aka tanada domin rabawa matasa masu shekaru 18 zuwa 40. Manufar shirin shine bunkasa sana’o’in hannu, da rage zaman kashe wando a tsakanin matasa, da karfafa hada-hadar tattalin arziki a tsakanin matasan Najeriya. Ga masu bukatar cike fom, zasu iya ta adreshin yanar-gizo dake kasa:
Tallafın karatun gaba da sakandire na NELFUND:
Wani asusu ne da gwamnatin tarayya ta samar don baiwa daliban Najeriya har 260,000 masu karamin karfı damar yin karatun ba tare da tsaiko ba saboda rashin wadata. A halin yanzu, an bada kimanin Naira biliyan 1.17 ga dalibai a sassa daban-daban na Najeriya, har yanzu ana cigaba da nema tare da bayarwa. Za a iya cike fom din ta yanar gizo a adreshin dake kasa:
Tallafın SUPA Initiative:
Wannan tallafı zai bada horo, lasisi da kuma jari ga masu sana’o’in hannu don kara inganta su. Shirin na SUPA Initiative zai shafi mutane miliyan goma a fadin Najeriya cikin shekara biyu. Zaku iya rejista ta yanar gizo-gizo akan adreshin dake kasa: