Sanarwar Ga Masu Neman Shiga Aikin Dan Sanda Na 2025

Hukumar kula da aikin ‘yan sanda na Kasa (POLICE SERVICE COMMISSION) karkashin jagorancin DIG Hashimu Argungu (mai ritaya), tare da hadin gwiwar rundunar ‘yan sandan Nigeria karkashin jagorancin IGP Kayode, za su debi sabbin kuratan ‘yan sanda.
Kamar yadda sanarwa ta zo, wannan karon babu batun cike takardan neman shiga aikin ‘yan sanda saboda karancin lokaci. Za a diba ne daga cikin wadanda suka taba neman shiga aikin har suka rubuta jarabawar Computer Based Tests (CBT) a ranar 5 da 6 ga watan Maris, shekarar 2024 amma basu samu nasarar samun aikin ba. Daga cikinsu za a diba.
A yanzu ana bukatar su shiga cikin wannan website É—in da za a bude zuwa nan da karfe 12 na ranar yau
https://apply.policerecruitment.gov.ng
Wanda ya ga sunansa sai ya yi printing invitation slip zuwa gurin da za a yi gwajin lafiya (medical screening) a Police Hospitals dake Zonal Headquarters guda 17 a fadin tarayyar Nigeria.
Za a fara medical screening nan da kwanaki hudu, wato ranar 26-2-2025, sannan a kammala zuwa ranar 12-3-2025. Wanda bai samu damar yin gwajin ba, shikenan ya wuce shi.
Ku taimaka wajen isar da wannan sakon domin ya isa ga ‘yan uwa musamman na kauyuka.
Allah Ya bawa mai rabo sa’a.