Abubuwan Da Suke Karawa Mace Ni’ima Hadida Dandano Wanda Zaki Sarrafasu Dakanki:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu mai albarka na arewamusix.com
Mafi yawancin mata rashin kula da kai da rashin sanin irin abubuwan da yakamata su dinga ci domin samun dauwamammiyar niāima a jikinsu da samun gamsuwar kawunansu da jin dadin mazajensu, shike haifar musu da matsalar daukewar niāima da kuma daukewar shaāawa gaskiya.
Abubuwan dasuka kamata mu mata mu dingacins, domin karuwar niāimar dake jikinmu:
Dafarko dai ana son mace ta dinga cin daya koh biyu daga cikin wadannan abubuwan kullum a rana, a cikinsu kuwa akwai abubuwa masu saukin kudi wanda duk rashin kudinki koh rashin halin maigida, zaki iya siya, kuma wadannan abubuwan suna kara lafiya da kuzari a jikkunan alāumma sannan kuma garkuwa ne ga kamuwa da wasu cutukan, haka kuma yana karawa mata niāima da jin dadi wajen mazajensu sosan Gaske
Ga Hadin Nan A Kasa:
- Kankana
- Ayaba
- Gwanda
- Goba
- Lemo
- Tumatir
- Rake
- Aya
- Kwakwa
- Dafafiyar gyada
- Zuma
- Nono
- Madara
- Madarar Shanu
- Gurji
- Dabino
- Chukwui
- Zogale
- Ruman
- Inibi
- Tuffa
- Zaitun.
Ga misali zan bayar, yau idan kika sami jikakkiyar ayarki kikaci, gobe ki samu rakenki kisha, jibi kuma ki samu nunannen tumatur dinki manya guda 2 koh 3 ki shanye, gata kuma kisha kankana koh nono, yakasance ki dinga cin abu kala koh biyu ne a cikinsu, toh wallahi Ina tabbatar miki banda niāima, hatta fatar jikinki sai ta murje ta goge tayi kyau.
Sannan kuma wasu daga cikin su a na shan ruwansu domin niāima ta musamman koh a sarrafa wani abin da ruwan, domin samun dauwamammiyar jin dadin maāaurata.
Ga kadan daga cikin yanda ake sarrafa wasu ruwan daga ciki:
- Ruwan Kankana sai ayaba manya guda 3 kankana kwata da tuffa, saiki hada ki markada ki zuba madarar ruwa gwangwani daya, zuma kuma yanda kikeso, ki saka kankara yayi sanyi, ku sha kamar juice keda maigidanki, wannan hadin yana karin niāima da kaurin maniyyi fiyeda yanda kuke zato.
- Ruwan Tumatir: shima ki markada tumatir guda biyu, ki zuba ruwan a cikin kwai guda 3, kisa magi da albasa ki soya ya yi ruwa-ruwa sai kici, shima yana saukar da niāima sosai da saka jin dadin auratayya, sannan yin hakan yana saka gogewar fata.
- Ruwan Kwakwa: Ki fasa kwakwarki ki tsiyaye ruwan Dake cikin kwakwar, sannan ki bare bakin bayan kwakwar ki goga kwakwar da āgreaterā, saiki markada a āblanderā, ki zuba ruwa a kan markadaddiyar kwakwar ki tace ruwan ki fidda dussar, toh da ma kin bare dabinonki a cikin gwangwanin madarar ruwa daya. Ki jika dabinon yayi laushi sai ki markada yayi laushi sosai, sannan saiki zuba a kan ruwan kwakwar, ki zuba ruwan da kika fasa kwakwar ya zubo a ciki, ki zuba zuma da garin madara cokali 3 a ciki, ki juyashi sosai, ki sa a fridge yayi sanyi koh kuma ki saka kankara, idan baki son sanyi sai ki sha a hakanshi, ki yini ki na sha kar ki barshi ya kwana. Hmmm tsumdum kenan! Amma ba zan ce komai ba, sai kin gwada kawai, ‘yar uwa zaki bada labari.
- Ruwan Zogale: Amfanin ruwan zogala ba zai lissafu ba a maganin cututtukan da yakeyi mana a jikinmu ba gaskiya. Amma zan yi bayanin kadan daga cikin amfaninshi a bangaren karin niāima a jikkunanmu ne.
- Ruwan Rake: Zaki bare rake ki yankashi gutsi-gutsi ki daka a turmi koh kuma ki markada a āblanderā ki na yi kina kara mishi ruwa a dissar raken kina matsewa, idan kin sami ruwan rake kamar cikin jog daya, sai ki sami ruwan tafasasshen baure jog daya, sannan sai ruwan jangari da jangagai da alewar mata da a ka tafasa su guri guda a tace su ma jog daya, sannan sai ki zuba wannan ruwayen naki a wuta ki zuba zuma kofi daya, kiyi ta dafawa har sai ruwan ya kone ya zama kamar cikin jug daya, toh sannan sai ki sauke. Amma zaki sa kaninfari da kayan kamshi a dahuwar. Idan ya huce sai ki juye a abu mai kyau, baya lalalcewa, kullum ki sha ludayi daya, zai ratsa jikinki ki sami dauwamammiyar niāima, maigida zai dinga jin dadinki ya na gamsuwa da ke sosai, wannan shi Ake kira da tsumin rake.
Don Allah ayi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.