Hanyoyi (5) Da Ma’aurata Zasubi Idan Har Basu Son Ciki Ya Shiga:
Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a wani sabon Shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafi namu Mai albarka na arewamusix.com
A yauma in shaa Allahu tafiya nake sauri-sauri domin na kawo muku yanda zakuyi idan har bakwason ciki ya shigeku.
Akwai wani babban likita daya kware a harkokin jima’i ‘Damian Avar’ wanda aka fi sani da ‘Sabi doctor’ da yake hira da PREMIUMTIMES ya ce kamata yayi duk ma’auratan da basu bukatan haihuwa da wuri toh su tanadi koh kuma suyi amfani da dabarun bada tazaran iyali da zai kare su daga daukan ciki na tsawon shekaru da dama.
Likitan ya bada wasu dabarun bada tazaran haihuwa guda 5 da ma’aurata zasu iya amfani dasu cikin kwanciyar hankali.
- Kororon roba wato (condom) a turance: Ana iya samun kororo raba a manya da kananun shagunan siyar da maganin dake kusa daku, sannan basu da tsada kuma amfani dasu yayin jima’i na hana mace daukan ciki tare da samar da kariya daga kamuwa da cututtukan zamani.
- Kwayoyi: Akwai kwayoyin bada tazarar haihuwa da ma’aurata zasu iya amfani dasu daban-daban wanda duk ake samu a kanana da manyan shagunan siyar da magunguna wato chemist koh pharmacy, su kwayoyin nada saukin kudi sannan kuma idan akayi amfani dasu yanda ya kamata yana hana mace daukan ciki.
- Cire Azzakari A Farjin Mace Lokacin Da Kaji Maniyyinka Zai Fito : Idan ma’aurata basu tanadi koh kuma basuyi amfani da dabarun bada tazaran haihuwa ba kuma basu son daukan ciki toh zasu iya amfani da dabaran zare azzakari kafin maniyi ya zuba cikin farjin mace, wannan dabaran bashi da inganci domin ma’aurata nayin kuka dashi cewa yana rage jin dadin jima’i, sannan kuma likita yace yin fitsari na taimakawa wajen fitar da maniyin dake dauke da kwayayen halitta wanda idan namiji ya shiga mace ba tare da yayi fitsari ba mace zata iya daukan ciki a wannan Lokacin.
- Wasa Da Junanku Har Ku Fitar Da Maniyyi: ma’aurata zasu iya wasa da juna ba tare da sun sadu/jima’i ba, saboda bincike ya nuna cewa wasa na cikin hanyoyin da suka fi gamsar da mace matuka ba sai an sadu da ita ba.
- Kada Ku Sadu A Lokacin Daukan Ciki: Bisa ga halitta akwai lokuttan da mata suka fi daukan ciki, hakan na faruwa ne bayan mace ta gama jinin haila wato jinin al’ada toh idan namiji ya fahimci haka zai iya kaurace wa matarsa har sai lokacin ya wuce koh kuma a yi amfani da kororon roba idan ya kama dole sai an sadu din.
Don Allah kuyi share wa sauran ‘yan uwa domin suma su amfana.