‘Yan Ashawo Romantic Story: Page 11 & 12

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafin namu mai albarka na arewamusix.com/

Page 1️⃣1️⃣ & 1️⃣2️⃣

Kuka mai cin zuciya Jiddo take yi tana rungume da kafafunta, yayin da Nazeefa take kokarin rarrashinta. “Jiddo, kiyi hakuri, komai ya riga ya faru. Yanzu babban abinda ya kamata mu mayar da hankali akai shine lafiyarki da kuma yadda zaki fara sabuwar rayuwa,” Nazeefa ta fada cikin sanyin murya.

A can gidan Tahreem kuwa, tana zaune a falo tana jiran dawowar Malam Dauda. Tana cikin wannan tunanin ne sai ga Malam Dauda ya shigo da sallama. “Hajiya, na dawo. Likita yace za’a iya sallamar yarinyar nan gobe idan har ta kara samun nutsuwa,” Malam Dauda ya sanar da ita.

Tahreem ta gyara zama, “To Malam Dauda, ina zamu kaita? Ba zamu iya barinta a asibiti ba, kuma bamu san kowa nata ba.” Malam Dauda ya yi shiru na dan lokaci, sannan yace, “Hajiya, tunda Nazeefa tana son yarinyar, me zai hana mu taho da ita nan gidan na dan lokaci?”

Tahreem ta harari Malam Dauda, “Nan gidan? Malam Dauda kana hauka ne? Ka san irin harkar da muke yi a nan gidan kuwa? Yarinya bafullatana ‘yar daji zaka kawo cikin wannan kazantar?” Malam Dauda ya sunkuyar da kansa, “Hajiya, ai Nazeefa tace zata kula da ita, kuma kinsan Nazeefa tana da tarbiyya.”

Washegari aka sallami Jiddo daga asibiti. Nazeefa ta kaita wani shago ta saya mata sabbin kaya da takalma. Jiddo sai rarraba ido take yi tana kallon motoci da gine-gine, komai na birni sabo ne a gare ta. Suna isa gidan Tahreem, Jiddo ta tsaya a bakin kofa ta ki shiga. Tsoron abinda zata tarar a ciki yake damunta.

Ku cigaba da bibiyanmu a arewamusix.com domin jin yadda zata kaya tsakanin Jiddo da sauran matan gidan Tahreem.

Leave a Comment