‘Yan Ashawo Romantic Story: Page 13 & 14

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafin namu mai albarka na arewamusix.com/

Page 1️⃣3️⃣ & 1️⃣4️⃣

Tsayawa Jiddo tayi a bakin kofar gidan Tahreem, tana kallon katon gidan da fentin sa yake ta kyalli. Nazeefa ta kamo hannunta, “Shigo Jiddo, nan ne gidanmu, karki ji tsoro kowa a nan mutunci zai miki.” Da kyar Jiddo ta daga kafa ta shiga falon, inda ta tarar da matan gidan su hudu zaune suna kallo.

Dukansu suka zuba mata ido, suna kallon yadda take rarraba ido kamar wadda aka jefo daga sama. Talatu ce ta fara magana, “Wacece kuma wannan Nazeefa? Daga ina kika samo wannan bafullatanar?” Nazeefa ta yi murmushi, “Wannan Jiddo ce, bakuwa ce a wajena, don Allah ku saki ranta.”

Tahreem ce ta fito daga dakinta tana kamshi, tana sanye da wata tsadaddiyar riga. Ta tsaya tana kallon Jiddo daga sama har kasa. “To, an riga an kawo ta kenan. Nazeefa, ki kaita dakin ki, ki nuna mata yadda ake amfani da bandaki da komai, bana son jin wari ko kazanta a falon nan.” Jiddo ta sunkuyar da kanta, tana jin wani irin kuncin zuciya.

A dakin Nazeefa, Jiddo ta zauna a kasa ta ki zama a kan gado. “Anty Nazeefa, me yasa mutanen nan suke kallo na haka? Ni fa tsoro nake ji, gwamma in koma daji na.” Nazeefa ta zauna kusa da ita, “Kiyi hakuri Jiddo, birni ne haka yake. Nan gaba zaki saba dasu, kuma zasu daina kallonki haka.”

Cikin dare, Jiddo ta kasa barci. Tana jin hayaniyar kade-kade da dariyar maza da mata daga falon gidan. Ta tashi ta labaro labule tana kallon yadda motoci suke ta shigowa gidan. Ta fara tunanin ko wane irin gida ne wannan? Kuma me yasa mutane suke ta shigowa cikin dare haka?

Ku cigaba da bibiyanmu a arewamusix.com domin jin asirin da Jiddo zata fara ganowa a gidan Tahreem.

Leave a Comment