Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafin namu mai albarka na arewamusix.com/
Page 1️⃣9️⃣ & 2️⃣0️⃣
Suna isa babban otal din, Jiddo ta kankame hannun Nazeefa, idanunta sun cika da tsoro yayin da take kallon hasken lantarki da kuma yadda mutane suke shiga da fita cikin shiga ta alfarma. Tahreem ce take gaba tana taku cikin takama, har suka isa wani daki na musamman (VVIP suite) inda wasu manyan mutane suke zaune.
Daya daga cikin mutanen, wanda ake kira Alhaji Sani, ya zuba wa Jiddo ido tun daga kofa. “Lallai Tahreem, wannan kam kin kwaso mana danyen nama. Wannan bafullatanar ta daban ce,” Alhaji Sani ya fada yana murmushin jin dadi. Jiddo ta sunkuyar da kanta, tana jin kamar kasa ta tsage ta shige saboda yadda mutumin yake kallonta.
Nazeefa tana tsaye a gefe, zuciyarta tana tafasa. Ta san cewa yau ne ranar da rayuwar Jiddo zata iya canjawa zuwa mummunar hanya. Ta yi kokarin magana amma Tahreem ta harare ta. “Jiddo, matso kusa da Alhaji mana, karki ji tsoro,” Tahreem ta fada tana tura Jiddo gaba.
Alhaji Sani ya kamo hannun Jiddo, wanda hakan ya sa ta razana ta ja baya da sauri. “Don Allah karka taba ni!” Jiddo ta fada cikin kuka. Falon ya yi tsit, kowa ya zuba mata ido. Alhaji Sani ya bata rai, “Tahreem, meye hakan? Ashe ba a koya mata tarbiyyar birni ba ne?” Tahreem ta shiga bashi hakuri tana rantsuwar cewa tsoron farko ne kawai.
Nazeefa ta kasa jurewa, ta matso ta kamo hannun Jiddo. “Hajiya, yarinyar nan ba zata iya ba. Don Allah mu tafi gida.” Tahreem ta kalli Nazeefa da wani irin kallo mai ban tsoro. “Nazeefa, idan kika sake kika bata min shirin nan, to ki sani yau ce ranar karshenki a gidan Tahreem.”
Ku cigaba da bibiyanmu a arewamusix.com domin jin yadda zata kaya tsakanin Nazeefa da Tahreem a kan Jiddo.