Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafin namu mai albarka na arewamusix.com/
Page 1️⃣5️⃣ & 1️⃣6️⃣
Washegari da safe, Jiddo ta tashi da wani irin nauyin zuciya. Ta fito daga dakin Nazeefa a hankali tana rarraba ido. Ta tarar da falon gidan ya yi kaca-kaca da kwalaben abubuwan sha da sauran tarkace, alamar an yi gagarumin biki a daren jiya. Wata yarinya ce take ta faman share gurin, tana ganin Jiddo ta yi mata wani kallo na raini.
“Ke bafullatana, me kike kallo? Ko kema an kawo ki ne ki fara harka?” yarinyar ta tambaya tana dariya. Jiddo ba ta fahimci me take nufi ba, sai kawai ta juya ta koma daki. Nazeefa tana fitowa daga wanka ta ga Jiddo a takure, “Jiddo, me ya faru? Wani ne ya taba ki?”
“Anty Nazeefa, me ake yi a gidan nan cikin dare? Na ga maza da mata suna ta hayaniya, kuma gidan duk ya baci,” Jiddo ta tambaya cikin rashin sani. Nazeefa ta yi shiru, ta kasa kallon idon Jiddo. “Jiddo, karki damu da abinda kike gani, kawai ki tsaya a dakina, zan dinga kawo miki duk abinda kike bukata.”
Tahreem ce ta shigo dakin, tana sanye da kayan bacci masu tsada. “Nazeefa, yau muna da baki na musamman daga Abuja. Kuma ina so ki shirya Jiddo, ina so su ganta. Irin wadannan ‘yan matan daji suna da daraja a wajen manyan mutane.” Nazeefa ta razana, “Haba Anty Tahreem, yarinyar nan fa ba ta san komai ba, kuma kinsan irin firgicin da ta shiga.”
“Ban tambayi ra’ayinki ba Nazeefa! Na fada miki tun farko, ba zan ciyar da mutum a banza ba. Ko dai ta shigo harka, ko kuma ta bar min gida ta koma dajin da kika kwaso ta,” Tahreem ta fada cikin fushi sannan ta fice. Jiddo ta kalli Nazeefa, “Anty Nazeefa, me take nufi? Wace harka ce zan shiga?” Nazeefa ta fashe da kuka, ta kasa ba Jiddo amsa.
Ku cigaba da bibiyanmu a arewamusix.com domin jin halin da Jiddo zata tsinci kanta a ciki.